Author: Kabiru Basiru Fulatan

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aike da sunan Mista Joseph Olasunkanmi Tegbe zuwa Majalisar Dattawa domin tabbatar da shi a matsayin sabon Ministan Lantarki na ƙasar nan. Wannan sanarwa tana ƙunshe ne a cikin wata takarda da Mai Magana da Yawun Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Alhamis, 30 ga watan Afrilu, 2026. HARIN FARM CENTRE: Kada A Bari Rikicin Siyasa Ya Lalata Tattalin Arzikin Kano — Abbas Ibrahim Naɗin na Tegbe ya biyo bayan murabus ɗin da tsohon Ministan Lantarki, Adebayo Adelabu ya yi, domin shiga takarar zaɓe. Waye Joseph Tegbe? Tegbe, wanda ɗan asalin Jihar…

Read More

Harin da wasu da ake zargin ’yan daba masu alaƙa da siyasa suka kai Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Cente da ke Kano ya janyo hankalin jama’a, inda ake ganin lamarin wata babbar barazana ce ga zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki a jihar, musamman yayin da ake tunkarar zaɓen 2027. ‎Lamarin ya faru ne a ranar Litinin, 27 ga Afrilu, 2026, inda aka ga yadda wasu suka mamaye kasuwar, suka yi sace-sace, tare da lalata dukiyoyi ciki har da motoci da babura. Haka kuma, mutane da dama sun samu raunuka a yayin harin. Kano: Gwamnati Ta Fara…

Read More

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da kammala shirye-shirye domin gudanar da bikin Ranar Ma’aikata ta shekarar 2026 cikin tsari mai kyau. Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin jihar, Hajiya Bilkisu Shehu Maimota, ce ta bayyana hakan a yayin wani taron shiri da ya haɗa da Kwamishinan Yaɗa Labarai, wakilan ƙungiyoyin ƙwadago da sauran masu ruwa da tsaki. Dangote na shirin gina katafariyar matatar mai a gabashin Afirka Ta ce gwamnati na da niyyar shirya biki mai armashi da zai nuna muhimmancin rawar da ma’aikata ke takawa wajen ci gaban jihar. A cewarta, kyakkyawar alaka tsakanin gwamnati da ƙungiyoyin ƙwadago na taimakawa wajen inganta…

Read More

Hamshaƙin attajirin nahiyar Afirka, Aliko Dangote ya bayyana shirin gina katafariyar matatar man fetur da za ta iya tace ganga 650,000 a kowace rana a gabashin Afirka. Yayin da yake jawabi a wani babban taron masu ruwa da tsaki kan masana’antun Afirka, da ke gudana a birnin Nairobin Kenya, Dangote ya ce shirin wani mataki ne na bunƙasa masana’antu a nahiyar. Kashi 70 na laifukan da ake aikatawa a Kano sanadin shaye-shaye ne – Ƴansanda Taron – wanda manyan shugabannin Afirka da masu zuba jari da masu ruwa da tsaki kan harkar masana’antu suka halarta – an shirya shi ne…

Read More

Wani rahoton ‘yansanda ya bayyana cewa sama da kashi 70 cikin 100 na manyan laifuka a Jihar Kano na da alaƙa da shan miyagun ƙwayoyi da fataucinsu, lamarin da ya nuna yadda matsalar ke da nasaba da rikice-rikicen daba da a yankin. Rahoton sirri da aka samu ya nuna cewa shan miyagun ƙwayoyi ya zama babban abin da ke ƙarfafa ƙungiyoyin daba, waɗanda ke shiga rikice-rikicen tashin hankali, hare-haren makamai da faɗace-faɗacen titi a sassan jihar. Rahotan, wanda rundunar ‘yansandan Jihar Kano ta tattara ƙarƙashin jagorancin kwamishinan ‘yansanda Ibrahim Adamu Bakori, ta nuna cewa an kama mutane 3,081 da ake…

Read More

A ƙalla mutane 12 ne suka mutu yayin da wasu kusan 38 suka jikkata sakamakon wata gobara da ta tashi bayan fashewar tankar mai a jihar Cross River da ke kudancin Najeriya. ‎ ‎Lamarin ya faru ne a ranar Laraba a ƙauyen Ndem, cikin ƙaramar hukumar Ogoja, a lokacin da ake aikin sauya mai daga wata tanka zuwa wata. Rahotanni sun ce tankar ta kife ta fada cikin wani kogi da ke kusa, kafin daga bisani ta kama da wuta, lamarin da ya haddasa gobara mai tsanani. ‎An tabbatar da naɗin Dr Muttaqha Darma a matsayin sabon ministan gidaje ‎Shaidun…

Read More

Majalisar Dattijan Najeriya ta tabbatar da naɗin Dakta Muttaqha Rabe Darma a matsayin ministan gidaje. Hakan ya biyo wasiƙar da shugaba Bola Tinubu ya aike wa Majalisar a Jiya, yana buƙatar ta amince da naɗin. A yayin zaman majalisar, wadda Shugaban majalisar Godswill Akpabio ya jagoranta, ƴan majalisar sun yi wa Dr Darma tambayoyi da dama kan dabarun da zai yi amfani da su wajen magance matsalar ƙarancin gidaje da ƙasar ke fama da ita. Bayan gamsuwa da amsoshin sa, Majalisar ta amince da naɗa shi. A ranar 21 ga watan Afrilun 2026 ne Shugaba Tinubu ya yi wasu sauye-sauye…

Read More

Majalisar dattawan Najeriya ta buƙaci gwamnatin ƙasar ta duba yiwuwar dakatar da yaƙin neman zaɓen 2027 a wasu jihohin arewa guda takwas da ke fama da matsalar tsaro. Sanata mai wakiltar Bauchi ta tsakiya Abdul Ningi ne ya gabatar da ƙudurin a zaman majalisar na ranar Alhamis, inda ya ce akwai buƙatar a duba yanayin tashe-tashen hankulan da ake fama da su a ƙasar. Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, Ningi ya ce bai kamata ƴan majalisar su kauda kai daga matsalar tsaron da ke damun wasu sassan ƙasar saboda su suna zaune a Abuja. “Mataki ne da ya zama…

Read More

Gwamnatin tarayya ta shigar da ƙarar tuhuma mai ƙunshe da laifuka 13 a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja kan wasu da ake zargi da shirya juyin mulki domin kifar da Shugaba Bola Tinubu kamar yadda jaridar TheCable ta rawaito. Daga cikin waɗanda ake zargin akwai tsohon Manjo Janar, tsohon Kyaftin na rundunar ruwa, wani jami’in ‘yan sanda mai aiki, da wasu mutum uku. Ana zarginsu da aikata laifukan tayar da yaƙi da ƙasa, cin amanar ƙasa da kuma ayyukan ta’addanci. A baya, rundunar tsaro ta tabbatar da cewa akwai shirin juyin mulki a shekarar 2025, inda aka kama…

Read More

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi zargin cewa akwai wani sabon shiri na haɗa shi da aikata laifuka domin sake tsare shi. A wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, ya fitar, ya bayyana cewa wannan yunkuri na daga cikin wani tsari na ɓata masa suna da kuma hana shi samun ‘yanci. Dole Najeriya ta samu tsaro – Babban hafsan tsaro Sanarwar ta kuma ce El-Rufai na duba yiwuwar ɗaukar matakin shari’a kan jaridar The Nation, bisa wani rahoto da ta wallafa da ke danganta shi da wani hari da aka kai…

Read More