Hadakar Malamai da Kungiyoyin Musulunci a Jihar Kano sun yi kira ga ‘yan siyasa da magoya bayansu da su guji kalaman tunzura jama’a tare da gudanar da harkokin siyasa cikin lumana domin kare zaman lafiya a jihar.
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta bayyana damuwa kan yadda ake samun zafafan kalamai da wasu dabi’u da ka iya haddasa tashin hankali a tsakanin masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa.
Ƙalubalen Da Masu Ƙananan Sana’o’i Ke Fuskanta Saboda Ƙarancin Wutar Lantarki A Kano
Kungiyar ta ce siyasa bai kamata ta zama hanyar haifar da rikici ko rarrabuwar kawuna ba, illa a mayar da hankali wajen gabatar da manufofi da shirye-shiryen ci gaban al’umma.
Hadakar ta kuma bukaci matasa da kada su bari a yi amfani da su wajen tayar da zaune tsaye ko aikata ayyukan da za su kawo cikas ga zaman lafiya da tsaron al’umma.
Ta kara da cewa al’ummar Kano suna da tarihi na zaman lafiya da mutunta juna, don haka akwai bukatar kowa ya ba da gudunmawa wajen tabbatar da dorewar wannan kyakkyawar al’ada.
Kazalika, kungiyar ta yaba da kokarin hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar.
Sanarwar ta samu sa hannun sakataren kungiyar, Dakta Sa’idu Ahmad Dukawa.
