A Jihar Kano: Yadda Tashin Gobarar Kasuwar Singer Ke K’ara Barazana Ga Ci Gaban Kasuwanci
Daga Abdullahi Yusuf tare da haɗin gwiwar Abbas Ibrahim, Mohammed Kabir Yau,Salisu Ibrahim Fagge , Mustapha Muhammad da Kabiru Fulatan
Kimanin sau biyu Gobara ta tashi cikin kankanin lokaci a Kasuwar Singer da ke birnin Kano. Wannan Gobara ta janyo asarar dukiya mai tarin yawa, inda aka kiyasta ta haura naira biliyan 20, lamarin da ya jefa daruruwan ’yan kasuwa cikin mawuyacin hali.
Gobarar dai ta faru ne a watan Fabrairun 2026, lokacin da kasuwar – wadda ake kallonta a matsayin daya daga cikin manyan kasuwannin kayayyakin masarufi a Kano – ta fuskanci gobara har sau biyu a gajeren lokaci.
Shugaban kungiyar ’yan kasuwar Singer, Barrista Junaidu Muhammad Zakari, ya bayyana cewa gobarar farko ta tashi ne daga wani babban rumbun ajiya da ke cikin MAZAF Complex a cikin tsakiyar kasuwar.
A cewarsa, gobarar ta lalata manyan rumbunan ajiya guda biyu tare da dukiyoyin da darajarsu ta kai biliyoyin naira.
Ya kara da cewa tsananin gobarar ya sa wani gini mai hawa biyu da ke kusa da wurin shi ma ya kama da wuta, daga bisani kuma ya rushe gaba daya, inda duk abin da ke cikinsa ya kone kurmus.
Kayayyakin da suka lalace sun hada da kayan abinci, sabulai, madara, kwalayen biskit da dai sauransu
Sai da Jami’an Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, da Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya, tare da rundunar kashe gobara ta Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano, suka yi hadaka wajen kokarin dakile gobarar.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a tabbatar da ainihin musabbabin gobarar ba, da yake ci gaba da barazana ga harkokin Kasuwanci a wannan katafariyar Kasuwa ba.
Wasu dai na hasashen cewa gobarar na iya kasancewa sakamakon solar da cunkoson kayayyaki a kasuwar ko kuma dalilin chakuduwar wasu sinadarai da ake ajiye da su a rumbunan kasuwar ne ya janyo rashin Gobarar.
Sai dai kuma, Kungiyar Renewable Energy Association of Nigeria (REAN) ta ja hankulan mutane da su guji yin gaggawar danganta gobarar da hanyoyin samar da wuta na solar da ke cikin Kasuwar.
A wata sanarwa da daraktan hulda da jama’a na kungiyar, Oisereime Lloyd-Dietake, ya sanyawa hannu, Kungiyar ta jajanta wa ’yan kasuwar da gobarar ta shafa, kuma ta ce, har yanzu hukumomi ba su tabbatar da musabbabin tashin gobarar ba.
.
Ana sa bangaren, Shugaban Hukumar Hada hadar Kasuwanci ta Kano watau KACCIMA, Ambasada Hamza Darma, ya kiyasta cewa asarar dukiya da aka yi ta kai kimanin naira biliyan 15.
A wani kiyasin kuma, shugaban kwamitin rabon tallafi ga wadanda gobarar ta shafa, Alhaji Umar Faruk Ibrahim, ya ce hasashen asarar ya haura naira biliyan 20.
Alhaji Umar Faruk Ibrahim, wanda kuma shi ne Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, ya ce gwamnatin tarayya ta bayar da tallafi na naira biliyan 5 domin tallafawa ’yan kasuwar da gobarar ta shafa, yayin da kuma Kungiyar Gwamnonin APC ta bayar da gudunmawar naira biliyan 5 a matsayin tallafi.
Bugu da kari, wasu ’yan Najeriya da suka tausaya wa lamarin sun bayar da gudummawar miliyoyin kudade domin tallafawa ga ’yan kasuwar.
Yayin da ake cikin wannan alhini, bincike ya nuna cewa mafi yawan ’yan kasuwar Singer ba su da inshorar kasuwanci.
Shugaban kasuwar, Barrista Zakari, ya ce tsauraran sharuddan kamfanonin inshora ne ya sa yawancin ’yan kasuwa ba su iya shiga cikin tsarin gudanar da inshora ba.
Matakan da gwamnatin Kano ke dauka
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ziyarci kasuwar domin jajanta wa ’yan kasuwar da gobarar ta shafa.
A yayin ziyarar, gwamnan ya sanar da bayar da naira miliyan 100 a matsayin tallafi ga wadanda gobarar ta shafa.
Haka kuma gwamnatin jihar ta amince da kashe sama da naira biliyan 3 domin fadada hanyoyin da ke kewaye da kasuwar, domin saukaka zirga-zirga da kuma inganta tsaro.
A halin yanzu dai jama’a da masana na kira ga hukumomi su gudanar da cikakken bincike domin gano ainihin musabbabin gobarar.
Wasu na ganin cewa gano hakikanin dalilin gobarar zai taimaka wajen daukar matakan da za su hana sake faruwar irin wannan bala’i a nan gaba a kasuwar Singer.
