Tsohon mataimakin gwamnan Jihar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
A cikin wata takardar murabus mai ɗauke da kwanan watan 29 ga Maris, 2026, wadda ya aikewa shugaban jam’iyyar a mazabarsa ta Gawuna da ke karamar hukumar Nassarawa, Gawuna ya ce matakin da ya dauka na barin jam’iyyar na son rai ne kuma na kashin kansa.
Gawuna ya sauka daga shugabancin kwamitin Gudanarwa na Bankin Lamuni na Tarayya.
Ya bayyana a cikin takardar cewa: “Ina sanar da ku a hukumance cewa na fice daga jam’iyyar APC daga ranar 29 ga Maris, 2026.”
Tsohon mataimakin gwamnan ya kuma gode wa jam’iyyar bisa damar da ta ba shi a lokacin da yake cikinta.
Gawuna, wanda shi ne dan takarar gwamna na APC a zaben 2023 a Kano, bai bayyana inda zai dosa a siyasance ba bayan ficewar tasa.
Ficewar tasa na zuwa ne a lokacin da ake ci gaba da sauye-sauyen siyasa a jihar Kano, gabanin zabukan gaba.
Wasu majiyoyi na kusa da shi sun ce ana sa ran zai gana da tsohon gwamnan jihar, Rabiu Musa Kwankwaso, a daren Litinin a gidansa da ke Miller Road.
