Gwamnatin tarayya ta shigar da ƙarar tuhuma mai ƙunshe da laifuka 13 a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja kan wasu da ake zargi da shirya juyin mulki domin kifar da Shugaba Bola Tinubu kamar yadda jaridar TheCable ta rawaito.
Daga cikin waɗanda ake zargin akwai tsohon Manjo Janar, tsohon Kyaftin na rundunar ruwa, wani jami’in ‘yan sanda mai aiki, da wasu mutum uku.
Ana zarginsu da aikata laifukan tayar da yaƙi da ƙasa, cin amanar ƙasa da kuma ayyukan ta’addanci.
A baya, rundunar tsaro ta tabbatar da cewa akwai shirin juyin mulki a shekarar 2025, inda aka kama wasu jami’an soji tare da ci gaba da bincike.
Haka kuma, iyalan waɗanda ake tsare da su sun bukaci a gurfanar da su a gaban kotu a fili tare da gaggauta shari’arsu, lamarin da ya kai ga gudanar da zanga-zanga a Abuja.
Ana sa ran za a ci gaba da shari’ar a gaban kotu domin tantance gaskiyar zarge-zargen.
