Nasiru Gawuna, jigo a jam’iyyar APC a Kano kuma Shugaban hukumar FMBN, ya ajiye mukaminsa.
Gawuna ya ce murabus ɗin nasa ya fara aiki nan take, kuma ya yi dai-dai da umarnin shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na cewa duk masu riƙe da mukaman siyasa su sauka gabanin wasu harkokin siyasa.
Shugaban NUJ Ya Yaba Da Aikin Kano Correspondents’ Chapel, Ya Kira ‘Yan Jarida Su Kara Hadin Kai
Ya godewa shugaban Ƙasa bisa damar da aka ba shi na yin aiki, inda ya bayyana cewa hakan wata babbar dama ce.
Rahotanni sun kuma nuna cewa Gawuna na shirin sauya sheƙa zuwa jam’iyyar ADC, yayin da ake ci gaba da sauye-sauyen siyasa gabanin zaɓen 2027.
