Kotun ƙolin Najeriya ta kori ƙarar da shugabancin PDP tsagin Tanimu Turaki ya shigar, inda yake ƙalubalantar matakin rushe taron zaɓen shugabanninsu da aka yi a Ibadan.
Yayin da yake sanar da matsayar alƙalan, mai shari’a Stepehen Adah ya bayyana cewa taron da suka gudanar a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamban 2025 a Ibadan rashin ɗa’a ne ga hukuncin babbar kotun tarayya da mai shari’a James Omotosho ya yanke inda ya dakatar da su daga gudanar da babban taron jam’iyyar.
Kotun ƙolin ta kuma soki ɓangaren Turaki game da zuwa kotun da ba ta da hurumi, a madadin zuwa kotun ɗaukaka ƙara.
Saboda haka, kotun ta tabbatar da hukuncin kotun ɗaukaka ƙarar da ta yanke na haramta taron PDPn a jihar Oyo.
Uku daga cikin alƙalai biyar ne suka amince da wannan hukuncin.
