Author: Kabiru Basiru Fulatan

Kungiyoyin goyon bayan jam’iyyar APC guda dubu ɗaya da ɗari biyar (1,500) da aka yi wa rajista sun amince da marawa shirin Renewed Hope Network (TRN) na Sanata Abdul’aziz Yari a matsayin wata kafa ta musamman da aka ƙirƙira domin wayar da kan jama’a domin tabbatar da sake zaɓen Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu karo na biyu a shekarar 2027. Wata sanarwa da Mataimakin Darakta Janar na gamayyar kungiyoyin, Dakta AK Peters, ya sanya wa hannu a Abuja, ta bayyana cewa bayan wani muhimmin taro, TRN ƙarƙashin jagorancin gogaggen mai wayar da kan jama’a na APC kuma tsohon Babban Mataimaki…

Read More

Gwamnatin Jihar Kano ta musanta rahotannin da ke cewa Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, zai jagoranci hawan Sallah mai zuwa a jihar. A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida  Ibrahim Abdullahi Waiya ya fitar, sanarwar ta ce rahoton da ke yawo a wasu kafafen yaɗa labarai da kuma shafukan sada zumunta ba shi da tushe. Jami’an tsaro Sun Dakile Yunƙurin Sace Ɗalibai A Kwalejin ’Yan Mata A Bauchi Ta bayyana cewa har yanzu ba a yanke wani hukunci a hukumance dangane da batun jagorancin hawan Sallah ba. Gwamnatin ta ƙara da cewa batun…

Read More

Jami’an tsaro a Jihar Bauchi sun dakile wani yunƙurin sace ɗalibai a Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnati (Government Girls’ College) da ke jihar, bayan wasu da ba a san ko su wanene ba sun yi ƙoƙarin shiga harabar makarantar. Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe huɗu na asubahin ranar Lahadi 15 ga watan Maris, lokacin da wasu mutane suka yi yunƙurin tsallaka katangar makarantar ta wani ɓangare da ke kusa da gidajen ma’aikata. Hatsarin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna ya jikkata mutane da dama Jaridar TheCable, wadda ta ruwaito rahoton daga majiyar tsaro Zagazola Makama,…

Read More

Fasinjoji da dama sun jikkata bayan wani jirgin ƙasa da ke jigila tsakanin Abuja zuwa Kaduna ya sauka daga layin dogo sakamakon cin karo da wani abu a kan hanyarsa. Lamarin ya faru ne yau Litinin a kusa da Asham a kan layin dogon da ke tsakanin Abuja da Kaduna, lamarin da ya jefa fasinjojin cikin fargaba. Kano: Kotu ta umarci matashi ya biya kuɗin maganin wanda ya jikkata Shugaban Hukumar Sufurin Jiragen Ƙasa (NRC), Kayode Opeifa, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an tura tawagar agajin gaggawa nan take bayan samun rahoton hatsarin. Binciken farko ya nuna…

Read More

Daga Abba Anwar  Akwai tunani daga mutane da yawa kafin zabubbukan da a ka gudanar na shugabannin jam’iyyar APC a jihar Kano da a ka gudanar kwanakin baya cewar, da wuya Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya iya gudanar da zabubbukan cikin nasara. Jama’a sun yi wannan tunanin ne ba wai dan shi Gwamnan bai jima da shigowa jam’iyyar ta APC ba ne. A’a an yi wannan tunani ne ta yin la’akari da irin rigingimun dake cike fal a jam’iyyar a jihar Kano. Ta gefe da gefe ta sama ta kasa, ta ko’ina ma. Kano: Kotu ta umarci matashi ya…

Read More

Kotun Shari’ar Musulunci ta Upper Sharia Court Shahuci da ke Kano, ƙarƙashin jagorancin Alƙali Abdu Abdullahi Wayyah, ta yanke hukunci kan wani matashi da aka samu da laifin dukan wani mutum har ya samu karaya. Kotun ta samu matashin mai suna Hassan Abba, mazaunin unguwar Durumin Iya – Lokon Maraba, da laifin kai wa wani matashi mai suna Ibrahim Haruna hari, lamarin da ya haddasa masa karaya a mukamuki. Bayanai da suka fito daga kotun sun nuna cewa wanda aka samu da laifin na daga cikin matasan da ake kira masu sukuwa da doki a bayan Gidan Sarkin Kano, duk…

Read More