Making ruwan sama da ambaliya ruwa sun yi sanadiyyar mutuwar mutane 107 da jikkata wasu 344, tare kuma da lalata ɗaruruwan gidaje tun daga ƙarshen watan Yuni zuwa yau a Pakistan.
Daga Zainab Kamal Ibrahim
Hukumar Kiyaye Afkuwar Iftila’i ta ƙasar NDMA, ta shaida wa manema labarai a ranar Lahadi cewa adadin mutanen da suka mutu sakamakon mamakon ruwan saman tun daga ƙarshen watan Yuni sun kai 107.
Adadin mutanen da su ka rasu a lardin Khyber Pakhtunkhwa ya kai 55, tare da mutane 36 a yankin Punjabi. Kuma fiye da rabin mutanen sun mutu ne sakamakon rushewar gidajen da su ke ciki.
Gwamnatin Bauchi Ta Musanta Rahoton Kayyade Sadakin Budurwa zuwa ₦3,000 Da Na Bazawara Zuwa ₦1,500
Jaridar Dawn ta ruwaito cewa hukumomin ƙasar sun samar da sansanoni guda 17 a birnin Lahore, domin zaunar da mutanen da su ka rasa muhallansu a sakamakon iftila’in.
Babbar Ministar Punjabi, Maryam Nawaz Sharif, ta bayyana cewa tuni hukumomin bayar da agajin gaggawa su ka bazama a dukkan yankunan domin gudanar da ayyukansu.
Inda hukumomin ƙasar su ka buƙaci al’ummar yankunan da su ci gaba da yin takatsantsan dangane da wuraren da za su shiga.
