Kamfanin Maltina ya ƙaddamar da wani shiri na wayar da kan ɗalibai kan muhimmancin karatun kimiyya da fasaha a makarantu 30 da ke faɗin Jihar Kano, domin ƙarfafa harkar ilimi da bunƙasa makomar matasa a jihar.
Wakilin kamfanin Maltina na Arewacin Najeriya, Kabiru Al-Kasim, ya bayyana cewa wannan ba shi ne karo na farko da kamfanin ke gudanar da irin wannan shiri a Kano ba, yana mai jaddada aniyar kamfanin na ci gaba da tallafa wa harkokin ilimi da ci gaban matasa.
Da yake jawabi a wajen taron, Malam Sagiru Umar Dan Bare daga Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano, ya ce shirin zai taimaka matuƙa wajen inganta harkar ilimi tare da ƙara wa ɗalibai ƙwarin guiwar mayar da hankali kan karatun kimiyya da fasaha.
Ya bayyana Kano a matsayin jiha mai tarihi da fice a harkar neman ilimi, yana mai cewa akwai buƙatar ci gaba da ƙarfafa matasa su rungumi ilimin zamani domin anfani da shi wajen ci gaban al’umma da ƙasa baki ɗaya
“A yau duniya ta karkata ne zuwa kimiyya da fasaha, saboda haka irin wannan shiri zai taimaka wajen wayar da kan ɗalibai su fahimci muhimmancin waɗannan fannoni wajen gina makomar su,” in ji shi.
Shi ma a nasa jawabin, wakilin kamfanin Maltina, Kabiru Sale, ya ce kamfanin ya ɗauki wannan mataki ne sakamakon yadda gwamnatin Jihar Kano ke nuna jajircewa wajen bunƙasa ilimi.
Ya ce manufar shirin ita ce ƙara wa ɗalibai fahimta kan muhimmancin ilimin kimiyya da fasaha domin gina kyakkyawar makoma tare da taimakawa ci gaban tattalin arziki.
A nasa ɓangaren, Hakimin Rimin Gado kuma wakilin Sarkin Kano, Alhaji Auwal Mudi Yakasai, ya yaba wa kamfanin Maltina bisa gudunmawar da yake bayarwa wajen bunƙasa ilimi da ci gaban al’umma a jihar.
Ya ce haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu na taka muhimmiyar rawa wajen samar da ci gaba mai ɗorewa a fannin ilimi da tattalin arziki a Kano.
