Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Da farko, ina miƙa godiya ta musamman ga Allah Maɗaukakin Sarki, wanda Ya ba mu damar kasancewa tare a wannan muhimmin taro na Ranar Ma’aikata ta Duniya ta shekarar 2026. Ina kuma taya dukkan ma’aikata a Jihar Kano, Najeriya da duniya baki ɗaya murna bisa wannan rana mai muhimmanci, wadda ke tunatar da mu irin rawar da ma’aikata ke takawa wajen gina al’umma mai dorewa. Hakika, ma’aikata su ne ginshiƙin ci gaban kowace ƙasa. Ba za a iya samun cigaba mai ma’ana ba tare da jajircewarsu, sadaukarwarsu, da ƙwazon aikinsu ba. Saboda…
Author: Kabiru Basiru Fulatan
Masu ƙananan sana’o’i a Jihar Kano na ci gaba da kokawa kan yadda ƙarancin wutar lantarki ke janyo musu asara tare da kawo cikas ga ci gaban harkokinsu a daidai lokacin da ake fama da tsadar rayuwa a faɗin ƙasar. Binciken Jaridar Inda Ranka ya nuna cewa yawan katsewar wutar lantarki ya tilasta wa masu sana’o’i, musamman masu ɗinki, masu walda da masu sana’ar sanyi, komawa amfani da janareta da sola domin ci gaba da gudanar da ayyukansu na yau da kullum. Aman Wuta: Sama da Mutane 5,000 Sun Tsere Daga Gidajensu a Philippines Sai dai, hauhawar farashin man fetur…
Tsohon ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Bichi, Hon. Mahmoud Baba Bichi, ya ayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar Sanatan Kano Ta Arewa a zaɓen 2027 karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC). Bichi ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyara sakatariyar jam’iyyar APC ta Jihar Kano, inda ya ce ya zo ne domin sanar da shugabannin jam’iyyar kudirinsa na neman kujerar majalisar dattawa. Samar da Aminci, Shi Ne Farko — Dole a Kawar Da Siyasar Dauka Makamai Daga Fagen Siyasar Kano Ya bayyana cewa tuni ya sayi fom ɗin tsayawa takara a hedikwatar APC ta ƙasa da ke…
Daga Comrade Abbas Ibrahim Yayin da Jihar Kano ke tunkarar wani muhimmin mataki a harkokin siyasa na Babban Zaɓen 2027, bukatar daukar matakan da suka dace domin kare rayuka, dukiyoyi da martabar dimokuradiyya na kara zama wajibi fiye da kowane lokaci. Haramta daukar makamai a wuraren tarukan siyasa ba zabin son rai ba ne, wajibi ne. Rikicin da ya faru a ranar Litinin, 27 ga Afrilu, 2026, a kusa da kasuwar Farm Centre dake Kano, ya sake fito da yadda tarukan siyasa ke iya rikidewa zuwa tashin hankali idan aka bar magoya baya ba tare da kulawa da takunkumi ba.…
DAGA ZAINAB KAMAL IBRAHIM Fiye da mutane 5,000 ne suka tsere daga gidajensu a ƙasar Philippines bayan da dutsen mai aman wuta Dutsen Mayon ya fara fitar da toka mai yawa, lamarin da ya jefa al’umma cikin fargaba. Rahotanni sun bayyana cewa dutsen da ke yankin Bicol ya fitar da gagarumar toka da ta mamaye sararin samaniya, lamarin da ya tilasta wa mazauna yankunan da ke kusa da shi barin gidajensu domin tsira da rayukansu. Yadda za a Fara Jigilar Maniyatta Aikin Hajji a Ƙasar nan. A cewar hukumomi, mutanen da abin ya shafa sun samu mafaka a sansanonin wucin…
Zainab Kamal Ibrahim A ranar Lahadin nan ne ake sa ran jirgin farko na maniyyata aikin Hajjin bana ta shekarar (2026) na ƙasar zai tashi zuwa Saudiyya arabiyya don gudanar da aikin Hajjin bana. Hukumar alhazan ta ƙasar nan NAHCON, ta ce an kammala dukkan shirye-shirye da Ake gudanarwa don gudanar da jigilar maniyyata cikin nasara. Hukumar ta ja hankalin maniyyatan ƙasar nan kan abubuwan da ya kamata su kiyaye, domin kauce wa matsala a ƙasar ta Saudiyya. Tin da fari, mataimakiyar Darakta Fatima Sanda Usara,ta ce a sashen yada labaran hukumar, ta ce kawo yanzu hukumar na ci gaba…
Sakataren Gwamnatin Jihar Kano (SSG), Alhaji Umar Faruk Ibrahim, ya ce bincike ya tabbatar da cewa kamfanonin bada bashi ne suka cire sama da Naira biliyan 1.5 daga albashin ma’aikatan jihar, ba tare da hannun jami’an gwamnati ba. Kano City Guide SSG ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin bikin ranar ma’aikata ta duniya da ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC suka shirya a Fadar Gwamnatin Kano. Amurka Ta Sanar Da Shirin Janye Sojojinta 5,000 Daga Jamus. Ya ce binciken da wani kwamitin gwamnati ya gudanar tare da haɗin gwiwar wani kamfanin bincike mai zaman kansa ya gano cewa…
DAGA ZAINAB KAMAL IBRAHIM Ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta sanar da cewa za ta janye dakarun soji kimanin 5,000 daga Jamus. Amurka ta yi barazanar janye sojojinta da ke ƙasashen Italiya da Spain. Wannan matakin ya zo ne a daidai lokacin da aka samu rashin jituwa tsakanin Shugaban kasan Amurika Donald Trump da sabon Shugaban Gwamnatin Jamus, Friedrich Merz. Donald Trump ya bayyana hakane bayan da Merz ya soki dabarun Amurka a yaƙin da take yi da Iran, inda ya bayyana cewa Iran ta kunyata Amurka a tattaunawar neman zaman lafiya. A kasar. Sai daii Shugaban kasar Amurika Trump…
DAGA ZAINAB KAMAL IBRAHIM Matatar man Dangote dake Najeriya ta sanar da dawo da wasu daga cikin ma’aikatanta na injiniyoyin da ta ladabtar da su wajen tura su aiki a wasu ma’aikatu, sakamakon wani laifi da suka yi a baya. Sanarwar da kamfanin dillancin labarai ya fitar ya ce dawo da waɗannan ma’aikata ya biyo bayan afuwar da akai musu bayan ɗaukar matakan ladabtarwa ta cikin gida. Kotun ƙoli ta kori ƙarar PDP ɓangaren Tanimu Turaki Jaridar The Cable ta wallafa cewaa ƙasar ta ɗauki matakin dawo da ma’aikata bakin aikin su, ya biyo bayan sanya hannu da kuma…
Kotun ƙolin Najeriya ta kori ƙarar da shugabancin PDP tsagin Tanimu Turaki ya shigar, inda yake ƙalubalantar matakin rushe taron zaɓen shugabanninsu da aka yi a Ibadan. Yayin da yake sanar da matsayar alƙalan, mai shari’a Stepehen Adah ya bayyana cewa taron da suka gudanar a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamban 2025 a Ibadan rashin ɗa’a ne ga hukuncin babbar kotun tarayya da mai shari’a James Omotosho ya yanke inda ya dakatar da su daga gudanar da babban taron jam’iyyar. Shugaba Tinubu ya aike da sunan Joseph Tegbe ga mjalisa don tantance shi a matsayin Ministan Lantarki Kotun…