DAGA ZAINAB KAMAL IBRAHIM
Ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta sanar da cewa za ta janye dakarun soji kimanin 5,000 daga Jamus.
Amurka ta yi barazanar janye sojojinta da ke ƙasashen Italiya da Spain.
Wannan matakin ya zo ne a daidai lokacin da aka samu rashin jituwa tsakanin Shugaban kasan Amurika Donald Trump da sabon Shugaban Gwamnatin Jamus, Friedrich Merz.
Donald Trump ya bayyana hakane bayan da Merz ya soki dabarun Amurka a yaƙin da take yi da Iran, inda ya bayyana cewa Iran ta kunyata Amurka a tattaunawar neman zaman lafiya. A kasar.
Sai daii Shugaban kasar Amurika Trump ya mayar da martani ta kafafen sadarwa inda ya soki Merz, inda yace, Bai San abinda yake fadaba gwamnatin sa ta kasa bayar da hadin Kai a yankin Iran.
Sanarwar ta fitone ta bakin mai magana da yawun Pentagon Sean Parnell ya fitar, ta cewa janyewar za ta ɗauki tsawon watanni 6 zuwa shekara 1 kafin a kai ga kammalawa, ya Kara dacewa KO da an janye a kwai sojojin Amurika kimanin 30,000 da zasu cigaba da Zama a Jamus.
Da ga nan Trump ya kuma yi barazanar janye sojoji daga ƙasashen Italiya da Sifaniya saboda ƙin amincewarsu da shiga yaƙin Iran.
