A sanarwar da mukaddashin shugaban hulɗa da jama’a na hukumar, Moyosola F. Adesina ya fitar daga hedikwatar WAEC da ke Yaba, ya ce an gudanar da jarabawar ne a cibiyoyi 166 a faɗin Najeriya daga 28 ga Janairu zuwa 14 ga Fabrairu 2026.
Jimillar ɗalibai 10,480 ne suka rubuta jarabawar, daga ciki dalibai 3,429 kashi 32.72% sun samu credit a akalla darussa biyar ciki har da Turanci da Lissafi.
An rantsar da Ali Musa Hardwoker a matsayin halartaccen shugaban karamar hukumar Kumbotso a Kano
Wannan ya nuna ƙaruwa da kashi 5.76% idan aka kwatanta da sakamakon shekarar 2025 wanda ya kai 26.96%.
Haka kuma, dalibai 43 masu buƙata ta musamman sun shiga jarabawar, inda WAEC ta ba da tallafi ga makafi 11, masu matsalar ji 4, da kuma albinos 4.
WAEC ta ce an riga an kammala duba sakamakon dalibai 8,418 (80.32%), yayin da sakamakon dalibai 2,062 ke kan dubawa saboda wasu kurakurai da suka fito daga wajen daliban.
Sai dai hukumar ta riƙe sakamakon dalibai 75 saboda zargin magudin jarabawa, kuma ana bincike akai kafin a yanke hukunci.
Hukumar ta shawarci dalibai su duba sakamakonsu a shafin yanar gizon WAEC, inda kuma za su iya samun kwafin takardar shaidarsu ta dijital.
