DAGA ZAINAB KAMAL IBRAHIM
Fiye da mutane 5,000 ne suka tsere daga gidajensu a ƙasar Philippines bayan da dutsen mai aman wuta Dutsen Mayon ya fara fitar da toka mai yawa, lamarin da ya jefa al’umma cikin fargaba.
Rahotanni sun bayyana cewa dutsen da ke yankin Bicol ya fitar da gagarumar toka da ta mamaye sararin samaniya, lamarin da ya tilasta wa mazauna yankunan da ke kusa da shi barin gidajensu domin tsira da rayukansu.
Yadda za a Fara Jigilar Maniyatta Aikin Hajji a Ƙasar nan.
A cewar hukumomi, mutanen da abin ya shafa sun samu mafaka a sansanonin wucin gadi, inda ake ba su agajin gaggawa yayin da ake ci gaba da kokarin share hanyoyin da toka ta rufe.
Tun da farko, kimanin mutane 500 ne aka fara ruwaito cewa sun tsere, sai dai daga bisani adadin ya karu zuwa sama da 5,000 sakamakon tsanantar aman wutar.
Masana sun ce Philippines na daga cikin ƙasashen da suka fi fuskantar iftila’o’i a duniya, saboda yawan duwatsu masu aman wuta, girgizar ƙasa, ambaliya da kuma zabtarewar ƙasa da ake yawan samu a yankunan ƙasar.
Hukumomi na ci gaba da sanya ido kan halin da ake ciki, tare da gargadin mazauna yankunan da ke kusa da Dutsen Mayon da su bi umarnin tsaro domin kauce wa haɗari.
