Ya mai girma Shugaban Karamar Hukumar Tarauni, Hon. Ahmad Sekure a matsayina na dan karamar hukumar Tarauni na rubuta wannan wasika ne saboda kira a gareka, a matsayin ka na shugaban al’umma wanda suka amince maka zama shugaban su domin suna da kyakkyawan yakinin cewa zaka musu adalci, kare rayuwar su, tallafa musu da ilimi da ayyukan yi.
Ina mai kira da jan hankali dangane da batun sauya fasalin daya daga cikin kasuwannin da suke karkashin kulawar karamar hukumar Tarauni wato kasuwar ‘Yar Kasuwa dake unguwar Gyadi-Gyadi kuma mazabar Gyadi-Gyadi Kudu wacce take mallakin daidaikun mutane ciki harda marayu da iyayensu suka mutu suka bar musu gado suke gudanar da kasuwanci a wannan kasuwa da cewa yunkurin da akeyi na sabunta kasuwar abune mai kyau. Amma saidai akwai bukatar duba na tsanaki wajen aiwatar da aikin. Dalili na kuwa anan shine.
1. RASHIN INGANTACCEN SHUGABANCI
Na Farko: Babu cikkakken hadin kai a cikin shugabancin kasuwar wanda yasa aka sami rabuwar kai tsakanin bangorori biyu (wadanda suka amince da kuma wadanda basu amince ba) saboda rashin samun cikkakken bayani dangane da yadda makomar mammalaka shagunan zai kasance.
2. BABU TAKARDAR YARJEJENIYA
Na Biyu: A cikin Korafe-korafe da akeyi wanda kasani akwai batu na rashin wata gamsasshiyar takarda daga karamar hukuma zuwa ga mammallaka shaguna kan cewa ga yadda yarjejeniya zata kasance. Sannan basuda masaniya akan kamfanin da zaiyi aikin, karamar hukuma ce kawai ta kawo shi ba tare da zama dasu ba (a cewar shugabancin kasuwar da suka amince da aikin)
3. BARAZANA GA MAMMALLAKA SHAGUNA
Na Uku: Wadanda aka wakilta su tattauna da masu shaguna suna musu barazanar cewa gwamnatin ka zata kwacewa duk wanda yaki amincewa da bukatar aikin.
4. RASHIN KYAKKYAWAN WAKILCIN MASU SHAGUNA
Na Hudu: Akwai har yanzu wadanda suke wakiltar masu shaguna ba tare sanin wasu daga cikin masu shagunan ba, wanda a bisa doka dole ne kowa yasan halin da ake ciki. (Wanda kuma kanada masaniya akan cewa akwai wadanda basu sani ba).
5. MAKOMAR MATASA SAMA DA 1000 DAKE SANA’A A KASUWAR
Na Biyar: Ka duba adadin matasan da suke neman abunci a cikin kasuwar wanda babu daya daga cikin su da gwamnati ta bawa aikin yi. Sune suka samarwa kansu mafita ba tare da tallafin gwamnati ba wanda sun haura akalla mutane 1000.
Saboda haka yakamata duk abunda za’ayi a duba maslahar al’umma domin saboda su aka samu damar kaiwa inda ake a halin yanzu. Kuma shugabanci yana dorewa ne kadai idan akwai adalci a cikin sa. Da fatan za’ayi nazari akan wannan muhimmin al’amari domin yin duba na tsanaki.
Nine naka
✍️ Musa Ado Musa
Mai Kishin Karamar Hukumar Tarauni
