DAGA ZAINAB KAMAL IBRAHIM
Gwamnan Jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, ya yi alkawarin samar wa sabon Babban Limamin Masarautar Ilorin, Sheikh Muhammad Bashir Dasuki Imam Fulani, sababbin motocin aiki na hukuma domin sauƙaƙa masa gudanar da ayyukansa na addini da jagoranci.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar girmamawa da ya kai wa sabon Babban Limamin a Ilorin ranar Talata, inda ya nemi addu’o’i domin zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaban Jihar Kwara.
Gwamnatin Kano Ta Fara Sabon Gangamin Rajistar Karin Zaɓe Yayin Da Wa’adi Ke Gabatowa
A cewar wata sanarwa da gwamnatin jihar ta wallafa, Gwamna Abdulrazaq ya samu rakiyar Kwamishinan Ilimi da Ci Gaban Jari-Hujjar Dan Adam, Lawal Olohungbe, tare da wasu manyan jami’an gwamnati da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa domin taya sabon Babban Limamin murnar nadinsa.
Yayin ziyarar, gwamnan ya bayyana nadin Sheikh Dasuki a matsayin wani muhimmin mataki na ƙarfafa haɗin kai da fahimtar juna tsakanin al’ummar Musulmi a jihar.
Ya ce zaɓen matashin malamin, wanda ya yi karatu a jami’o’in Azhar, ya nuna hangen nesa da hikimar shugabancin masarautar wajen tabbatar da ci gaba, haɗin kai da bai wa kowa dama.
Gwamnan ya kuma yi addu’ar Allah Ya ba sabon Babban Limamin kariya, lafiya da tsawon rai domin ci gaba da yi wa addini da al’umma hidima cikin nasara.
Haka zalika, ya yi kira ga al’ummar Masarautar Ilorin da daukacin mutanen Jihar Kwara da su bai wa sabon jagoran addinin cikakken goyon baya wajen sauke nauyin da aka ɗora masa.
An sanar da nadin Imam Fulani mai shekaru 42 a matsayin Babban Limami na 13 na Masarautar Ilorin a ranar 10 ga watan Yuni, ta bakin Mataimakin Sarkin Ilorin kan harkokin yaɗa labarai, Abdulraheem Murtala.
Bayan sanar da nadin, Gwamna Abdulrazaq ya taya Mai Martaba Sarkin Ilorin, Ibrahim Sulu-Gambari, murna, yana mai bayyana zaɓen a matsayin alamar hikima da kyakkyawan tsari a tafiyar masarautar.
A nasa bangaren, wasu fitattun malaman addinin Musulunci da suka hada da Sheikh Abdulkadir Oba Sholagberu da Sheikh Sohibul Bayan sun yaba wa gwamnan bisa irin gudunmawar da yake bayarwa wajen tallafa wa cibiyoyin addini da shugabannin addini a jihar.
