Tsohon mataimakin gwamnan Kano kuma tsohon ɗan takarar gwamnan jihar a jam’iyyar APC ya karɓi katin jam’iyyar ADC a hukumance, a ranar Litinin.
A ranar Lahadi ne ya sanar da ficewa daga jam’iyyar APC, tare da jadadda mubaya’arsa ga tsarin Kwankwasiyya.
Gawuna Ya Fice Daga Jam’iyyar APC
Bayanai na cewa komawar tasa na da alaƙa da rashin yadda ake zargin mayar da shi saniyar ware a jam’iyyar APC.
Tundai bayan da kotun koli ta Najeriya ta tabbatar wa da Abba Kabir Yusuf kujerar gwamnan Kano, wasu magoya bayan Nasiru Gawuna suka yi ta sa ran shugaba Tinubu zai bai wa mai gidan nasu mukami mai girma.
A ranar Asabar ne Gawuna ya sanar da ajiye mukamin shugaban hukumar gudanarwa na bankin lamunin gidaje na Najeriya da Tinubu ya yi masa.
