A Jihar Kano da ke arewacin Najeriya, aƙalla mutane 10,000 masu cancantar kaɗa ƙuri’a ne suka yi rajistar katin zaɓe a wani babban shiri na kwanaki shida da aka gudanar a jihar. Shirin, wanda aka tsara domin ƙarfafa rajistar masu jefa ƙuri’a, ya samu halartar jama’a da dama, lamarin da masu shirya shi suka ce ya nuna yadda al’umma ke ƙara fahimtar muhimmancin shiga harkokin dimokuraɗiyya. Kano: Indabo Ta Haskaka Ayyukan Gwamnatin Abba Kabir Yusuf Kwamitin da ke kula da shirin ya bayyana cewa sakamakon da aka samu ya zarce hasashen da aka yi tun farko, inda dubban matasa da…
Author: Kabiru Basiru Fulatan
A Kano, mai bai wa gwamna shawara kan wayar da kai da haɗa kan al’umma, Hajiya Bilkisu Yakubu Indabo, ta bayyana cewa gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na ci gaba da aiwatar da muhimman ayyuka da suka shafi ilimi da lafiya, tare da ƙoƙarin ƙarfafa hulɗa da jama’a. Ta ce daga cikin nasarorin da aka samu akwai gyaran makarantu a sassa daban-daban na jihar, da kuma ɗaukar nauyin karatun ɗalibai zuwa ƙasashen waje domin inganta harkar ilimi. Haka kuma, ta bayyana cewa gwamnatin ta fara ɗaukar nauyin kula da lafiyar mata masu juna biyu a dukkan ƙananan hukumomin jihar, a…
Mai bai wa Gwamnan Kano shawara kan wayar da kai da haɗa kan al’umma, Hajiya Bilkisu Yakubu Indabo, ta ƙaddamar da wani shiri na musamman da nufin fito da nasarorin da gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta samu tare da ƙarfafa hulɗa da jama’a a faɗin jihar. An tsara gudanar da taron ne a ranar Litinin, 6 ga Afrilu, 2026, a ɗakin karatu na Murtala Muhammad Library, inda za a gabatar da cikakken bayani mai tushe kan ayyukan da gwamnatin ta aiwatar tun bayan hawanta mulki. INEC Ta Yi Gargadi Kan Yin Rijistar Katin Zaɓe Sau Biyu Indabo ta bayyana…
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sake gargadin jama’a da su guji yin rijistar katin zaɓe fiye da sau ɗaya, tana mai cewa hakan laifi ne da ke da hukunci mai tsauri a ƙarƙashin dokar zaɓe. Jami’ar hulɗa da jama’a ta hukumar, Hajiya Nahila Bello Dandago, ce ta bayyana hakan yayin wata tattaunawa a gidan rediyon Kano a ranar Asabar. Ta ce duk wanda aka kama da aikata irin wannan laifi na iya fuskantar ɗaurin kurkuku ko tara, ko ma duka biyun. Gwamnatin Kano Ta Tura Dalibai 550 Domin Taimakawa Wajen Faɗaɗa Rajistar Katin Zaɓe A Fadin…
Gwamnatin Jihar Kano ta tura dalibai 550 daga cibiyoyin ilimi tara domin taimakawa wajen faɗaɗa rajistar rajistar masu zaɓe CVR, a wani yunƙuri na ƙara ƙarfafa shiga harkokin dimokuraɗiyya a faɗin jihar. Shugaban Kwamitin Ƙarfafa Rajistar Masu Zaɓe na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da shirin a filin wasanni na Kofar Mata, inda ake gudanar da babban aikin rajistar masu zaɓe. Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Abbas Ibrahim, Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai, ya fitar a madadin Kwamitin Ƙarfafa Rajistar Masu Zaɓe na Jihar Kano. A cewar Waiya, an horas da…
A Jihar Kano, an ƙaddamar da wani shiri na kwanaki shida na rajistar Katin zaɓe, a wani yunƙuri na ƙara yawan masu katin zaɓe da kuma ƙarfafa shiga harkokin dimokuraɗiyya. Shugaban Kwamitin Ƙarfafa Rajistar Masu Katin Zaɓe na jihar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya jagoranci ƙaddamar da shirin a ranar Laraba a cibiyar wasanni da ke Kofar Mata. A cewarsa, an tanadi rumfunan rajista guda 20 domin sauƙaƙa wa jama’a yin rajista cikin gaggawa da kuma rage cunkoso. Waiya ya bayyana gamsuwarsa kan yadda jama’a suka fito domin yin rajistar, yana mai cewa hakan na nuna fahimtar al’umma kan…
A Jihar Kano, ana ci gaba da nuna damuwa kan yadda wasu masu anfani da shirin kula da lafiya na Hukumar KACHMA, ke fuskantar matsaloli wajen samun magunguna, duk da kasancewarsu cikin tsarin. Shirin kula da lafiya na Hukumar KACHMA tsari ne na taimakekeniya domin tallafawa masu rauni, musamman mata da tsofaffi, domin samun kulawa ta musamman. Bankin CBN Ya Fitar Da Sunayen Bankuna 33 Da Suka Cika Ƙa’idar Ƙara Jarinsu Rahotanni sun nuna cewa, matsalar gudanar da shirin ta fi shafar mata da tsofaffi marasa lafiya. Wakilanmu sun lura da cewa, matsalar ta fi k’amari a asibitin K’wararru na…
Babban Bankin Najeriya CBN ya fitar da sunayen bankuna 33 da ya amince cewa jarinsu ya kai su ci gaba da gudanar da hada-hada a cikin ƙasar, a wani yunƙuri na kare dukiyoyin abokan hulɗarsu. Cikin wata sanarwa da CBN ya fitar a jiya Laraba, ya ce shirin wanda aka soma tun watan Maris na shekarar 2024, an kammala shi a yanzu bayan shafe watanni 24 ana yinsa, domin ƙarfafa tsarin hada-hadar kuɗi tsakanin bankuna da abokan hulɗarsu a Najeriya. Babban bankin ya ce bankunan 33 da aka amince dasu sun samar da jari na Naira tiriliyan 4 da biliyan…
Tsohon mataimakin gwamnan Kano kuma tsohon ɗan takarar gwamnan jihar a jam’iyyar APC ya karɓi katin jam’iyyar ADC a hukumance, a ranar Litinin. A ranar Lahadi ne ya sanar da ficewa daga jam’iyyar APC, tare da jadadda mubaya’arsa ga tsarin Kwankwasiyya. Gawuna Ya Fice Daga Jam’iyyar APC Bayanai na cewa komawar tasa na da alaƙa da rashin yadda ake zargin mayar da shi saniyar ware a jam’iyyar APC. Tundai bayan da kotun koli ta Najeriya ta tabbatar wa da Abba Kabir Yusuf kujerar gwamnan Kano, wasu magoya bayan Nasiru Gawuna suka yi ta sa ran shugaba Tinubu zai bai wa…
Tsohon mataimakin gwamnan Jihar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC). A cikin wata takardar murabus mai ɗauke da kwanan watan 29 ga Maris, 2026, wadda ya aikewa shugaban jam’iyyar a mazabarsa ta Gawuna da ke karamar hukumar Nassarawa, Gawuna ya ce matakin da ya dauka na barin jam’iyyar na son rai ne kuma na kashin kansa. Gawuna ya sauka daga shugabancin kwamitin Gudanarwa na Bankin Lamuni na Tarayya. Ya bayyana a cikin takardar cewa: “Ina sanar da ku a hukumance cewa na fice daga jam’iyyar APC daga ranar 29 ga Maris, 2026.”…