Babbar kotun jihar Kano ƙarƙashin mai Shari’a Farida Dan Baffa, ta yankewa Shu’ibu Abdulkadir, hukuncin kiss ta hanyar rataya mazaunin unguwar Farawa a ƙaramar hukumar Kumbotso, bayan ta same shi da laifin kashe Rumaisa Shuaibu mai shekaru 22 a duniya
Daga Zainab Kamal Ibrahim
An gurfanar da wanda ake zargin a ranar 23 ga Agustan 2025, kan laifin kisan kai, laifin da ya saɓa da Sashe na 221 na Dokar Penal Code, kamar yadda kafar yada Labarai ta Daily Nigeria ta ruwaito.
A yayin shari’ar, masu gabatar da ƙara sun gabatar da shaidu uku tare da hujjoji da suka haɗa da bidiyon yadda aka aikata laifin, bayanan furuci da wanda aka yanke wa hukuncin ya rubuta, hotunan mamaciyar, wuƙar da aka yi amfani da ita wajen kisan da kuma wayarsa ta hannu.
An Gano Gawar Ɗalibin Jami’a A Cikin Tafkin Ruwa A Gombe
Kotun ta ce hujjojin sun tabbatar ba tare da shakka ba cewa Shuaibu ya kashe Rumaisa bayan ta ɗauki ciki daga gare shi, lamarin da ya sa aka yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Da yake martani kan hukuncin, Babban Lauyan Jihar Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru Maude, SAN, ya ce hukuncin ya nuna ƙudirin Ma’aikatar Shari’ar jihar na tabbatar da adalci, kare haƙƙin waɗanda aka zalunta da kuma hukunta masu aikata manyan laifuffuka.
Barrista Abdulkarim ya kuma yaba wa lauyan gwamnati Barr. Basiru Kabiru Aliyu bisa ƙwarewa da jajircewarsa wajen gudanar da shari’ar sa Yadda ya kamata.
