Author: Abdullahi Yusuf

SIYASAR KANO Lallai kam, yanzu Kano, birninta da kauyukanta, tudu da kwarinta,ta dauki Harami da Gangami na hada-hadar Siyasa,gabanin Babban Zaben shekarar 2027,wato badi ke nan. Tun farkon watan Janairu a ka fara ganin alamun dumamar yanayin Siyasar Kano,har zuwa ranar 23 ga shi wannan wata,wadda a cikinta ne Maigirma Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf,ya fita daga Jam’iyyar NNPP, kuma bayan kwanaki uku da yin hakan,wato ranar 26 ga watan Janairu,ya koma Jam’iyyarsa ta ainahi, wato APC. Wannan mataki da Maigirma Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf,ya dauka,ya kawo karshen duk wasu jita-jita da hasahe da a ka dade…

Read More

KAN DAKALI Muna masu farin cikin gabatar muku da Dandamalinmu na sharhi a kan al’amuran Yau Da Kullum mai suna,”Kan Dakali.”Mun samo wannan suna ne daga “Dakali” wanda wani abin zama ne da a ke ginawa a kofar gidan Malam Bahaushe,inda mutane suke ke taruwa a kansa su na hira, musamman ma da dare. A KAN DAKALI, wanda zai rika fitowa lokaci-lokaci a cikin wannan Jarida ta mu mai albarka,za mu rika yin tsokaci a kan al’amuran yau da kullum da su ka shafi zamantakewa,siyasa,tattalin arziki da sauransu,ba tare da nuna son zuciya, son kai,ko wani bangaranci ba. Mun gode.…

Read More