KARIN MAGANARMU NA YAU: In ka ji ana Ki Gudu,Sa Gudu ne bai zo ba.
Author: Abdullahi Yusuf
GIOPPINI Ta Yi Karin Haske Kan Rahoton Kananan Yara Masu Gararamba A Titunan Kano Daga Abdullahi Yusuf Babban Daraktan Global Improvement of Less Privileged Persons Initiative (GIOPPINI), Mohammed Ali Mashi, ya ce rahoton da aka fitar kan yawan Kananan Yara Masu Gararamba A Titunan Kano ba shi da nufin bata sunan gwamnati ko haifar da sabani. A cewarsa, kalaman da ya yi sun kasance ne domin jawo hankalin mahukunta kan matsalolin da ke bukatar kulawa, musamman halin da wasu yara marasa galihu ke ciki. Mashi ya bayyana cewa wasu daga cikin yaran na kwana a karkashin gada ko yawo a…
KARIN MAGANARMU NA YAU: Ta na jika,Kunamar Mai Gyambo.
KARIN MAGANARMU NA YAU: An daki Biri da rani,ya ce:”Laifin ba na yanzu ba ne.”
Fiye da Kananan Yara Miliyan Biyu Ke Gararamba A Titunan Kano — NGO Daga Abdullahi Yusuf Wata ƙungiya mai zaman kanta ta bayyana damuwa kan yadda yawaitar kananan yara masu rayuwar titi ke ƙaruwa a Kano, inda ta ce adadinsu ya haura miliyan biyu. Ƙungiyar Global Improvement of Less Privileged Persons Initiative (GIOPPINI) ta ce binciken da ta gudanar ya nuna cewa dubban yara na kwana a tituna da wuraren jama’a a kowace rana, cikin yanayi mara tsafta da rashin tsaro. Babban Daraktan ƙungiyar, Mohammed Ali Mashi, ya shaida wa manema labarai cewa da dama daga cikin…
KARIN MAGANARMU NA YAU: Banza ba ta yin Rogo,in ba a sha jira ba,a sha shinge.
KARIN MAGANARMU NA YAU: Dan Akuya ya je barbara, ya dawo da ciki.
KARIN MAGANARMU NA YAU: Dole ne,cin Kasuwa da Makiyi.
KARIN MAGANARMU NA YAU: Kaza ta yi “ya “ya a Rijiya,ba bu rabon Shaho bare Kare.
Kwamitin Kula Da Tashoshin Mota Ya Mika Gurbatattun Kwayoyi Na N1.5bn Ga Hukumar DMCSA Ta Jihar Kano Daga Abdullahi Yusuf Kwamitin Kula Da Tashoshin Mota na Jihar Kano ya mika gurbatattun kwayoyi da ya kwace na kudi kimanin N1.5b ga Hukumar Samar Da Magunguna Ta Jihar Kano,wato DMCSA,domin adana su, kafin a batar da su. Wannan labari ya na kunshe ne a cikin wata sanarwar da Jami’in Hudda da Jama’a na Hukumar ta DMCS,Farouk Isa Musa,ya bayar. Yayin da ya ke mika kwayoyin, Shugaban Kwamitin,Manjo Adamu Abubakar Usman mai ritaya, ya ce, kwayoyin wadanda su ka hada da na bogi…