Gwamna Abba Ya Rungumi Akidar “Kano First” Bayan Fatali Da Tsarin Kwankwasiyya Da Ya yi; Abin Da Ya yi Siyasa ce ko Sabon Tsari? Daga Abdullahi Yusuf, Mohammed Kabir Ya’u,Salisu Ibrahim, Abbas Ibrahim,Mustapha Muhammad,Kabiru Fulatan A jihar Kano, muhawara na ci gaba da ƙara zafi kan matakin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ɗauka na sauya sheƙa daga jam’iyyar New Nigeria People’s Party NNPP zuwa All Progressives Congress APC, tare da ƙaddamar da wata sabuwar manufa mai taken “Kano First”. Matakin dai ya zo ne a wani lokaci da ake ci gaba da fuskantar sauye-sauye a siyasar…
Author: Abdullahi Yusuf
Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka Daga Mohammed Kabir Ya’u, Abdullahi Yusuf, Abbas Ibrahim,Salisu Ibrahim,Mustapha Muhammad,Kabiru Fulatan Sabbin matakan da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dauka na fara shirin tsige Mataimakin Gwamna, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ba shakka sun tayar da gagarumin rikici na siyasa, kace-nace tare da kara zurfafa rashin jituwa tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da tsohon jagoransa na siyasa, Dr Rabiu Musa Kwankwaso. An tabbatar da cewa akalla ‘yan majalisa 38 ne suka rattaba hannu kan takardar neman tsige mataimakin gwamnan bisa zargin aikata manyan laifuka, amfani da mukami ba bisa ka’ida ba da kuma…
RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki Daga Abbas Ibrahim, tare da gudummawar Kabiru Fulatan; Abdullahi Yusuf; Salisu Ibrahim; Mustapha Muhammad da Muhammad Ya’u Rundunar Kano Neighbourhood Watch Security Corps, wadda gwamnatin Jihar Kano ta kafa domin tallafawa hukumomin tsaro a matakin al’umma, ta fara samun tasiri duk da cewa ba ta jima da fara aiki ba. Rundunar ta fara aiki a hukumance a ranar 23 ga Disamba, 2025, kuma a cikin watanni uku da suka gabata, jami’anta sun fara taka rawa a fannoni kamar tattara bayanan…
KARIN MAGANARMU NA YAU: Kowa ya sha Inuwar Gemu,bai kai Wuya ba.
A Jihar Kano: Yadda Tashin Gobarar Kasuwar Singer Ke K’ara Barazana Ga Ci Gaban Kasuwanci Daga Abdullahi Yusuf tare da haɗin gwiwar Abbas Ibrahim, Mohammed Kabir Yau,Salisu Ibrahim Fagge , Mustapha Muhammad da Kabiru Fulatan Kimanin sau biyu Gobara ta tashi cikin kankanin lokaci a Kasuwar Singer da ke birnin Kano. Wannan Gobara ta janyo asarar dukiya mai tarin yawa, inda aka kiyasta ta haura naira biliyan 20, lamarin da ya jefa daruruwan ’yan kasuwa cikin mawuyacin hali. Gobarar dai ta faru ne a watan Fabrairun 2026, lokacin da kasuwar – wadda ake kallonta a matsayin daya…
KARIN MAGANARMU NA YAU: Ido ba ya mutuwa Kwalli ya tashe shi.
KARIN MAGANARMU NA YAU: Mai tsoron Ruwa a Kwano,ba zai shiga Rijiya ya sha ba.
KARIN MAGANARMU NA YAU: Kowa ya hau Motar Kwadayi, to kuwa zai sauka a Tashar Wahala.
KARIN MAGANARMU NA YAU: Idan Tsuntsu ya ciwo danko,sai ya lika wa Dan Uwansa.
KARIN MAGANARMU NA YAU: Duk Dan da ya hana Uwarsa barci,shi ma ba zai runtsa ba.