Author: Kabiru Basiru Fulatan

‎Hukumar gudanarwar Jami’ar Northwest University Kano (NWUK) ta amince da korar dalibai 34 daga jami’ar bayan samunsu da hannu a laifukan da suka shafi satar amsa lokacin jarabawa. ‎Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Abubakar Ibrahim ya sanya wa hannu a madadin Magatakardar jami’ar, Dr. Adm. Isyaku Adamu. ‎Sanarwar ta bayyana cewa, an yanke wannan hukunci ne a yayin taron hukumar gudanarwar jami’ar karo na 66 da aka gudanar a ranakun 17 da 18 ga watan Yunin 2026, lokacin da ake nazarin sakamakon jarabawar zangon karatu na biyu na shekarar karatu ta 2024/2025. ‎ ‎Ta ce an dauki…

Read More

Shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago a Jihar Kano sun sake jaddada aniyarsu ta mara wa gangamin Rajistar Masu Zaɓe Ta Dindindin (CVR) baya, tare da yin kira ga ma’aikata da sauran ‘yan ƙasa masu cancantar kaɗa ƙuri’a da su yi rajista domin samun Katin Zaɓe na Dindindin (PVC). An bayyana hakan ne a wani taron wayar da kai da Ƙaramin Kwamitin Ƙwadago na Kwamitin Aikin Rajistar Masu Zaɓe Ta Dindindin (CVR) na Jihar Kano ya shirya, domin ƙarfafa gwiwar ma’aikata su shiga aikin rajistar da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ke gudanarwa. Da yake jawabi a taron, Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya…

Read More

Ƙungiyoyin farar hula masu yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Jihar Kano sun yi kira ga gwamnati, iyaye, malamai da sauran masu ruwa da tsaki da su haɗa kai domin daƙile matsalar shaye-shaye, wadda suka bayyana a matsayin babbar barazana ga makomar matasa da ci gaban al’umma. An bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin gangamin wayar da kai na “My Voice Against Drugs Walk”, da aka shirya domin bikin Ranar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Duniya, ranar da Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) ta ware a duk shekara domin wayar da kan al’umma kan illolin…

Read More

Daga Abbas Ibrahim Kafa Kwamitin Musamman Kan Yaƙi da Shan Miyagun Ƙwayoyi da Fataucin Su da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi, na ɗaya daga cikin matakan da suka zo a daidai lokacin da jihar ke ƙara fuskantar barazanar  shaye-shaye da fataucin miyagun ƙwayoyi ke yi ga tsaro, lafiya da makomar matasa. A tsawon shekaru, Kano na ci gaba da fama da matsalar shan miyagun ƙwayoyi, musamman a tsakanin matasa. Duk da irin muhimmancin da jihar ke da shi a matsayin cibiyar kasuwanci a Arewacin Najeriya, hakan ya kuma sa ta kasance cikin wuraren da masu safarar miyagun…

Read More

Kwamitin Kartakwana a kan Katin Zaɓe (CVR) a Jihar Kano ya buƙaci limaman masallatan Juma’a da su ƙara himma wajen wayar da kan al’umma kan muhimmancin mallakar katin zaɓe da kuma shiga cikin harkokin dimokuraɗiyya. ‎ ‎Wannan kira ya fito ne yayin wata ganawa da kwamitin ya yi da limaman masallatan Juma’a, inda Shugaban Ƙaramin Kwamitin Hulɗa da Malamai, Sheikh Ibrahim Abubakar Tofa, ya jaddada muhimmancin rawar da malamai ke takawa wajen isar da saƙonnin da suka shafi ci gaban al’umma. ‎ ‎Sheikh Ibrahim Abubakar Tofa ya bayyana cewa malamai na da tasiri mai girma a cikin al’umma, don haka…

Read More

DAGA ZAINAB KAMAL IBRAHIM  Tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na ƙasa, Uche Secondus, ya bayyana damuwarsa kan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke na soke rajistar wasu jam’iyyun siyasa, yana mai gargadin cewa hakan na iya yin illa ga tsarin dimokuraɗiyyar jam’iyyu da dama a Najeriya. A ranar Litinin ne kotun da Mai Shari’a Peter Lifu ke jagoranta ta umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ta soke rajistar jam’iyyun ADC, Action Peoples Party (APP), Action Alliance (AA), Accord Party da Zenith Labour Party (ZLP), bayan ta yanke hukuncin cewa jam’iyyun sun gaza cika wasu sharuddan kundin…

Read More

DAGA ZAINAB KAMAL IBRAHIM Gwamnan Jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, ya yi alkawarin samar wa sabon Babban Limamin Masarautar Ilorin, Sheikh Muhammad Bashir Dasuki Imam Fulani, sababbin motocin aiki na hukuma domin sauƙaƙa masa gudanar da ayyukansa na addini da jagoranci. Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar girmamawa da ya kai wa sabon Babban Limamin a Ilorin ranar Talata, inda ya nemi addu’o’i domin zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaban Jihar Kwara. Gwamnatin Kano Ta Fara Sabon Gangamin Rajistar Karin Zaɓe Yayin Da Wa’adi Ke Gabatowa A cewar wata sanarwa da gwamnatin jihar ta wallafa, Gwamna Abdulrazaq ya…

Read More

Gwamnatin Jihar Kano ta ƙara kaimi wajen wayar da kan jama’a da ƙarfafa masu cancantar kaɗa ƙuri’a su yi rajistar zaɓe, yayin da wa’adin kammala Rajistar Zaɓe ta Dindindin (CVR) da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanya ya rage ƙasa da makonni biyar. Shugaban Kwamitin Wayar da Kai Kan Rajistar Zaɓe ta Dindindin a Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Wa’iya, ya ce an samar da dabaru da tsare-tsare na musamman domin tabbatar da ƙarin jama’a sun shiga aikin kafin ranar 10 ga watan Yuli da za a rufe rajistar. Wa’iya, wanda kuma shi ne Kwamishinan Yaɗa Labarai…

Read More

Shugaban Kwamitin Wayar da Kan Jama’a Kan Rajistar Masu Zaɓe na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya sanar da kafa kwamitoci 12 na musamman domin ƙara kaimi wajen wayar da kan jama’a su yi rajistar zaɓe tare da karɓar Katin Zaɓe na Dindindin (PVC). Waiya ya bayyana hakan ne a yayin ƙaddamar da kwamitocin, inda ya ce matakin ya zama dole domin ci gaba da riƙe matsayin da Kano ke da shi na kan gaba a ƙasar nan wajen yawan masu yin rajista a ƙarƙashin shirin Rajistar Masu Zaɓe Ta Kullum (CVR) na Hukumar INEC. Ya ce an tsara…

Read More

Majalisar Ƙoli ta Shari’a a Najeriya (SCSN) ta bayyana matuƙar damuwarta kan yadda matsalar tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a sassa daban-daban na ƙasar nan, inda ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakan gaggawa da za su kawo ƙarshen kashe-kashe, sace-sacen mutane da sauran ayyukan ta’addanci da suka addabi al’umma. A cikin wata sanarwa da Sakatare Janar na majalisar, Malam Nafiu Baba Ahmad, mni, ya fitar a ranar 7 ga Yuni, 2026, SCSN ta ce ‘yan Najeriya na ci gaba da fuskantar rahotannin kashe-kashe, garkuwa da mutane, hare-haren ‘yan ta’adda da sauran munanan laifuka kusan a kowace rana, duk kuwa…

Read More