Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kai ziyarar dubiya ne da kuma ganin yadda su kansu ma’aikatan asibitin suke kulawa da lafiyar al’ummar jihar Kano. Ziyarar ta Gwamnan ta kasance ne a ranar juma’a cikin dare, a Irin bazatan da ya saba yi zuwa asibitocin gwamnati domin ganin yadda ake kulawa da lafiyar al’umma a wannan lokacin. Bayan gwamna Abba Kabir Yusuf ya gama duba mara sa lafiya, kuma ya kewaye kowanne ɓangare na asibitin tare da rakiyar likitan dake kan aiki tare da ma’aikatansa a wannan daren. Gwamnan kuma ya yaba da yadda yaga ma’aikatan wannan asibiti kwararru na Best…
Author: Kabiru Basiru Fulatan
Sarkin Shanu, Sarkin Maganin Gargajiya na Jihar Kano, Dr. Abubakar Yusuna, ya gayyaci al’umma zuwa shagalin Maulidin Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammad , da za a gudanar a Kano. A cikin sanarwar gayyatar da ya fitar, Dr. Abubakar Yusuna ya ce an shirya shagalin ne domin tunawa da haihuwar Annabi Muhammad , tare da bayyana muhimmancin koyi da kyawawan ɗabi’u da koyarwar Manzon Allah. Sanarwar ta ce za a fara gudanar da shagalin ne daga yau Juma’a, 1 ga watan Rabi’ul Awwal, wanda zai ci gaba har izuwa 30 ga watan Rabi’ul Awwal. Za a gudanar da babban taron ne a…
Kanal Mohammed Ma’aji, wani jami’in Sojin Najeriya da ake zargi da hannu wajen shirya wani yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ce abin da ya sa ya shiga cikin shirin shi ne kishin ƙasa da damuwa kan halin da Najeriya ke ciki, ba neman mulki ko wata fa’ida ta kashin kai ba. Daga Zainab Kamal Ibrahim Ma’aji ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da bayanansa kan zargin yunkurin juyin mulkin, inda ya ce matsin tattalin arziki, rashin ingantaccen shugabanci da kuma tabarbarewar jin daɗin ’yan Najeriya da jami’an tsaro sun taimaka wajen haifar…
Wani rahotan hukumar da ke ƙididdige yawan jama’a na duniya ya sanya Kano a matsayi ta 9 cikin biranen da suka fi yawan jama’a a duniya. Daga Zainab Kamal Ibrahim Birnin ya shiga sawun birane da suka haɗa da Shanghai da Beijing da Shenzhen da Chengdu dake ƙasar China, sai kuma Delhi da Mumbai a ƙasar India da kuma Kinshasa a Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo da Karachi a ƙasar Pakistan. Gwamna Abba Kabir Ya Amince Da Karin Albashi Ga Ma’aikatan Jami’o’in Kano Guda Biyu Waɗannan alƙaluma na Kano ana hasashen cewar na iya kaiwa miliyan 20 nan da…
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya amince da aiwatar da sabon tsarin karin albashi ga malaman jami’a da sauran ma’aikatan Jami’ar Aliko Dangote ta kimiyya da fasaha da ke Wudil, da kuma Jami’ar Northwest da ke cikin garin Kano. Daga Zainab Kamal Ibrahim Sabon tsarin albashin ya samo asali ne daga sabon tsarin biyan albashin da gwamnatin tarayya ta fara amfani da shi a jami’o’in gwamnatin tarayya. Daga Ranar Da Aka Zaɓe Ni Zan Soke Dokar Fanshon Gwamnoni A Kano Ibrahim Little Ɗan Takarar Gwamna A Jam’iyyar ADC Sanarwar da kakakin gwamnan jihar Sunusi Bature Dawakin Tofa,…
Ɗan takarar gwamnan Jihar Kano na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Alhaji Ibrahim Ali Amin Little, ya bayyana cewa zai soke dokar da ta bai wa tsofaffin gwamnoni damar karɓar fansho da wasu alawus-alawus, idan aka zaɓe shi a matsayin gwamnan jihar a 2027. Daga Zainab Kamal Ibrahim Little ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a Kano, yayin wani taron manema labarai, inda ya kuma sanar da zaɓen Abdulkadir Shehu Bari daga Ƙaramar Hukumar Rogo a matsayin abokin takararsa na mataimakin gwamna. ShugabaTunubu Ya Umurci EFCC Ta Bude Asusun Bankin Gwamnatin Jihar Osun Da Ta Kulle Ya…
Hukumar ICPC ta ce ba ta samu wata hujja da ke nuna cewa Femi Gbajabiamila, shugaban ma’aikatar fadar shugaban ƙasa, ya aikata laifi a cikin badakalar wata hukumar gwamnati ta bogi ba. Daga Zainab Kamal Ibrahim Hukumar ta ce mutumin da ya yi ikirarin cewa shi ne darakta janar na Presidential Foreign Investment Promotion Council, Prince Adeniyi Adeyemi, ba gwamnatin tarayya ta naɗa shi ba, kuma takardar naɗin da ya gabatar ta kasance jabun takarda ce. ICPC ta kuma ce hukumar da Adeyemi ke ikirarin jagoranta ba a taɓa kafa ta da wata doka ko umarnin gwamnati ba.…
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tunubu ya umurci Hukumar EFCC da ta gaggauta komawa kotu domin janye umarnin da ta samu na dakatar da asusun gwamnatin jihar Osun. Daga Zainab Kamal Ibrahim A cikin wata sanarwa da ya fitar, Tunubu ya ce ko da yake bai saba tsoma baki cikin ayyukan hukumomin yaki da cin hanci ba, ya damu da lokacin da aka bijiro da matakin ba, kasancewar jihar Osun na gab da gudanar da zaben gwamna. Muna Da Ikon Dakatar Da Asusun Gwamnatin Jiha Har Na Tsawon Sa’o’i 72 Kafin Umarnin Kotu. EFCC Shugaban ya ce bai san…
Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arziki zagon ƙasa (EFCC) ta ce matakin da ta dauka na dakatar da asusun Gwamnatin Jihar Osun ya yi daidai da tanadin doka. Daga Zainab Kamal Ibrahim Daraktan hulda da Jama’a na hukumar, Wilson Uwujaren,ya bayyana cewa an dauki matakin ne bayan gano wasu mu’amala da ya tada zargi a asusun cikin makon da ya gabata, kuma ba sai an samu umarnin kotu ba kafin yin hakan. WAEC Ta Rike Sakamakon Jarrabawar Dalibai 167,486 Ya ce dakatarwar ta shafi asusu guda daya kacal ne, ba wai an daskarar da dukkan asusun Gwamnatin…
Hukumar Shirya Jarrabawar Ƙasashen Yammacin Afirka (WAEC) ta sanar da riƙe sakamakon ɗalibai 167,486 da suka rubuta jarabawar kammala makarantar sakandare ta WASSCE ta shekarar 2026, sakamakon zargin hannu a maguɗin jarrabawa. DAGA ZAINAB KAMAL IBRAHIM Hukumar ta ce adadin da aka riƙe sakamakonsa ya kai kashi 8.59 cikin ɗari na jimillar ɗaliban da suka zauna jarabawar, wadda aka gudanar ta hanyar amfani da kwamfuta (CBT). Sai dai WAEC ta bayyana cewa wannan adadi ya ragu idan aka kwatanta da kashi 9.7 cikin ɗari da aka samu a shekarar 2025. NSCDC Ta Hukunta Jami’ai 79 Tare Da Sallamar 37…