Hukumar tsaro da kare fararen hula ta Najeriya (NSCDC) ta sanar da hukunta jami’anta 79 saboda laifuffuka daban-daban da suka haɗa da cin hanci, damfarar aikin yi, sata, sakaci, da karya ƙa’idojin aiki. DAGA ZAINAB KAMAL IBRAHIM Daga cikin jami’ai 37 da aka sallame su daga aiki, yayin da wasu ke fuskantar shari’a da hukuncin ritaya ta dole. Babban kwamandan NSCDC, dakta Ahmed Audi, ya ce cikin waɗanda aka sallama akwai jami’ai biyu na rundunar Mining Marshals da aka samu da laifin gudanar da aiki ba tare da izini ba, lamarin da ya haddasa mutuwar kwamandansu a…
Author: Kabiru Basiru Fulatan
Hukumar kula da Harkokin Ɗalibai Masu yi wa Ƙasa Hidima (NYSC), ta gargaɗi masu shirin fara hidima kan cewa ba za a ba su damar farawa ba har sai sun samu tantancewa daga Cibiyar Rajistar Tattara Bayanai ta Laturoni ta Ƙasa (NERD). Daga Zainab Kamal Ibrahim Rahotanni sun bayyana cewa, gargaɗin na zuwa ne yayin da hukumar take cigaba da shirin karɓar tawagar ɗalibai na sabon rukuni yayin da take kuma ɗaukar matakan tabbatar da tsaronsu yayin tafiye-tafiye zuwa sansanoninsu. Da yiwuwar haramta sana’ar Adaidaita Sahu da baburan haya a wasu sassan Abuja – Wike A wata sanarwa da…
Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana cewa ma’aikatar babban birnin tarayya Abuja na duba yiwuwar haramta zirga-zirgar baburan haya (Okada) da Adaidaita Sahu (Keke Napep) a wasu sassan tsakiyar birnin Abuja saboda matsalolin tsaro. Daga Zainab Kamal Ibrahim Wike ya ce matakin ya biyo bayan shawarwarin kwamitin tsaro na FCT, bayan rahotannin sirri sun nuna cewa masu aikata laifuka na amfani da babura wajen gudanar da ayyukansu. Ya ce an umarci hukumomin tsaro su tantance wuraren da za a hana zirga-zirgar babura da Adaidaita Sahu, tare da amincewa da samar da kayan aiki domin ƙarfafa…
Ana zargin wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da wasu matafiya da ke cikin tawagar rakiyar amarya daga garin Sheme na Jihar Katsina zuwa Jihar Kebbi, lamarin da ya sake nuna ƙalubalen tsaro a hanyoyin Arewa maso Yamma. Daga Zainab Kamal Ibrahim Rahotannin sun ce lamarin ya fito ne ta bakin mai ba da rahotanni kan harkokin tsaro a yankin Arewa maso Yamma, Bakatsine, wanda ya wallafa a shafinsa na X cewa tawagar ta faɗa hannun ’yan bindiga ne yayin tafiyarsu zuwa Jihar Kebbi domin rakiyar amarya. Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai…
Wasu kansiloli biyu na Ƙaramar Hukumar Fagge da ke Jihar Kano sun zargi Shugaban Ƙaramar Hukumar, Alhaji Salisu Usman Masu, da hannu wajen shirya harin da wasu da ake zargin ’yan daba ne suka kai musu bayan wani taro da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya halarta. Daga Zainab Kamal Ibrahim Kansilan ’Yanmata Gabas, Shamsu Ali Umar, da Kansilan Fagge D1, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Ƙaramar Hukumar, Sani Muhammad, sun ce lamarin ya faru ne a harabar Asibitin Cutar Masu Yaɗuwa (IDH) bayan kammala taron da gwamnan ya halarta a ranar Litinin. Matar Babban Jami’in Kuɗaɗen ISWAP…
Rundunar Sojin Nijeriya ta ce matar wani babban jami’in kula da harkokin kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP tare da ɗanta mai shekara 11 sun miƙa wuya ga dakarun Operation Haɗin Kai a ƙauyen Kusuma da ke Jihar Borno. Daga Zainab Kamal Ibrahim A cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labaran rundunar na riƙo, Kyaftin Mohammed Goni, ya fitar a ranar Asabar, ya ce bincike ya nuna cewa mijin matar, wanda shi ma babban kwamandan ISWAP ne, ya miƙa wuya tun ranar 25 ga Yuli. Haɗin Gwiwar Gwamnati Da Ƙungiyoyin Fararen Hula Zai Haɓaka Ci Gaban Kano – Bilkisu Indabo Sanarwar…
Mai Bai wa Gwamnan Jihar Kano Shawara ta Musamman kan Harkokin Wayar da Kai, Hajiya Bilkisu Yakubu Indabo, ta bayyana cewa gwamnatin jihar na shirin ƙaddamar da wani tsari na haɗin gwiwa da ƙungiyoyin fararen hula domin ƙara inganta aiwatar da shirye-shiryen ci gaba da kuma kusantar da su ga al’umma. Shirin mai suna Government–NGO Handshake na da nufin samar da kyakkyawar alaƙa tsakanin hukumomin gwamnati da ƙungiyoyin fararen hula, domin ƙarfafa wayar da kan jama’a, inganta gaskiya da riƙon amana, tare da bai wa al’umma damar shiga cikin shirye-shiryen raya jihar. A cewar Bilkisu Indabo, ƙungiyoyin fararen hula za…
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta ce ta ƙwato na’urorin hasken rana (solar) guda 160 da darajarsu ta kai kimanin Naira miliyan 59.2, waɗanda ake zargin wani magidanci mai shekaru 43 ya sace tare da ɓoye su a wani kango da ke unguwar Haye, cikin yankin Sharaɗa. Daga Zainab Kamal Ibrahim Kakakin rundunar ya bayyana cewa nasarar ta samu ne a wani samame da jami’an ’yan sanda suka gudanar bayan samun sahihan labarai na sirri, inda aka gano tare da ƙwato kayayyakin da ake zargin an sace. GECCI Ta Bukaci Gwamnati Ta Inganta Manufofin Kiwo Domin Tallafa Wa Makiyaya…
Hukumar Gandun Daji tare da haɗin gwiwar ƙungiyar Global Environment and Climate Conservation Initiative (GECCI) sun gudanar da taron bita na kwana ɗaya kan hanyoyin da gwamnati za ta bi wajen samar da ingantattun manufofi da za su bunƙasa harkokin kiwo da inganta rayuwar makiyaya a Najeriya. Daga Zainab Kamal Ibrahim Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban ƙungiyar GECCI, Abdulhamid Tahir Hamid, ya ce an shirya bitar ne domin duba yadda za a yi amfani da ilimin gargajiya tare da haɗa shi da sabbin dabarun kiwo domin inganta rayuwar makiyaya, kare muhalli da kuma tabbatar da tsaron…
Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) reshen Jihar Kano ta roƙi ma’aikatan gwamnati da su kwantar da hankalinsu tare da yin haƙuri kan jinkirin da aka samu wajen biyan albashin wasu ma’aikata, sakamakon wata matsalar fasaha da ta afku a bankin da ke kula da biyan albashin. Shugaban NLC na Kano, Kwamared Kabiru Inuwa, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce matsalar ta faru ne yayin sarrafa albashin ma’aikata. Ya ce kuskuren ya sa wasu ma’aikata suka karɓi albashinsu sau biyu, yayin da bankin ya cire ƙarin kuɗin da aka tura musu bisa kuskure. Haka kuma,…