Kasuwannin Dabbobi A Kano Na Ƙara Bunƙasa, Amma Amfani da “Sha Ka Fashe” Na Barazana Ga Lafiyar Jama’a —Rahoto Daga Salisu Ibrahim Fagge tare da haɗin gwiwar Abbas Ibrahim, Mohammed Kabir Yau, Abdullahi Yusuf, Mustapha Muhammad da Kabiru Fulatan Kasuwancin dabbobi a Kano na kara bunƙasa cikin sauri, yayin da buƙatar nama, madara da fata ke ƙaruwa a sassan Najeriya. Amma duk da wannan ci gaba, wani bincike na musamman ya nuna cewa ana fuskantar babbar barazana ta ɓoye wajan yawaitar amfani da wani sinadarin magani da ake kira “Sha Ka Fashe.” Binciken ya gano cewa…
Author: Abdullahi Yusuf
KARIN MAGANARMU NA YAU: Kowa ya raina tsaiwar Wata,ya hau sama ya gyara.
KARIN MAGANARMU NA YAU: Cin dare daya, kumburin ciki.
KARIN MAGANARMU NA YAU: Wainar Wake,kadan a ke cin ta,duk wanda ya ci ta da yawa,sai ta bata masa ciki.
KARIN MAGANARMU NA YAU: Gobara daga Rafi,maganinta Allah.
KARIN MAGANARMU NA YAU; Wuta tallan Turmi,in ka sayar kaya,in ma ba ka sayar ba,kaya.
Kano Ta Yi Cikar Kwari “Ta Dabo Sha Baki;Ta Dabo Tumbin Giwa;Kamisulu Alfun; Mai Mata Mai Mota, Mai Tumaki Mai Jakai; Yaro Ko Da Me Ka Zo An Fi Ka;Kano Garin Zaman Lafiya Da Walwala.” Wadannan duk kirarin Kano ne.Allah Ya albarkanci wannan Gari da ke Kudu da Sahara. Yanzu ne fa Kano ta ke shan Baki,har ma a na ganin cewa ta sha su har iya wuya, saboda irin mutanen da ke yin tururuwa zuwa cikinta daga ko ina cikin kasar nan, musamman ma Jihohin Arewa, na kusa da na nesa. Daga cikin mutanen da ke shigowa cikin Kano…
KARIN MAGANARMU NA YAU: Banza ba ta kai Zomo Kasuwa.
KARIN MAGANARMU NA YAU: Ja da baya ga Rago,ba tsoro ba ne,shirin fada ne.
KARIN MAGANARMU NA YAU: Ja da baya ga Rago,ba tsoro ba ne,shirin fada ne.