KARIN MAGANARMU NA YAU Mai hankali shi ke bai wa Kaza ruwa da damina
Author: Abdullahi Yusuf
KARIN MAGANARMU NA YAU Abin rabo ne,wai Makocinka ya biya wa Matarka kudin zuwa Hajji.
KARIN MAGANARMU NA YAU An ce da Raggo sha Fura ka tafi gona,ya ce,”ai kun raba mini hankali.”
KARIN MAGANARMU NA YAU An sayar da gonar Rago an sai masa Fura, sai ya ce,”haka ta fi,” Matarsa kuma ta ce,”Allah Ya sa Furar a dame ta ke.”
Karin Maganarmu Na Yau: Daki ya rufta da Gurguwa da Dan Autan gida,ta ce,”dole ne a zo.”
Karin Maganarmu Yau: Daki ya rufta da Gurguwa da Dan Autan Gida,ta ce,”dole a zo.”
Karin Maganarmu Na Yau: An ce da Kuturu Allah Ya la’ance shi,sai ya ce,”sau nawa kuma?”
Karin Maganarmu Na Yau: Allah Mai mutantani,in ji Jaba ta ga bakin Mijinta.
Karin Maganarmu Na Yau: Wai an ce da Gwauro yaya Iyali,ya ce,”Zancen ku ke so.”
Karin Maganarmu Na Yau: An ce da Makaho ga ido,ya ce,”Wari ya ke yi.”