KARIN MAGANARMU NA YAU: Kowa ya yi zagi a Kasuwa,ya san da wanda ya ke.
Author: Abdullahi Yusuf
KARIN MAGANARMU NA YAU: Zakara a rataye,ba ya cara.
KARIN MAGANARMU NA YAU: Banza a banza zuwa fadar Kurege,da gudu ya je,da gudu ya dawo.
KARIN MAGANARMU NA YAU: Maraya ba ya aure,idan gari akwai Munafukai.
KARIN MAGANARMU NA YAU: Yanzu na ji baka, wai Da ya harbi Ubansa.
KARIN MAGANARMU NA YAU: Da arziki da da tashin hankali, gara tsiya da kwanciyar hankali.
KARIN MAGANARMU NA YAU: Mai Kaza a Aljihu,ba ya jimirin Aasss!
KARIN MAGANARMU NA YAU: Kwadayi, Kwadayi, Kwadayi ma kas Kare.Wai Kare ya gano Kashi,Kura kuma ta gano Karen,sai Kare bai dauki kashin ba,har Kura ta wuce da Karen.
KARIN MAGANARMU NA YAU: Idan dai Amarya ba ta hau Doki ba,to kuwa ba a dora mata Kaya ba.
KARIN MAGANARMU NA YAU: Idan ka ji Makaho ya ce a yi wasan jifa,ya taka dutse ne.