Karin Maganarmu Na Yau: Komai karfin tusa,ba ta hura wuta.
Author: Abdullahi Yusuf
Kanfanin Dangote Ya Hada Gwiwa Da Kamfanin Honeywell Don Fadada Matatar Mai Daga Abdullahi Yusuf Kamfanin Dangote ya hada gwiwa da Kamfanin Honeywell International Inc don tallafawa wajen aiwatar da kashi na gaba na fadada Matatar Mai ta Dangote. A karkashin wannan hadin kan, za a samar da wata babbar fasaha da za ta sanya Matatar Man ta rika tace danyen man fetur ganga miliyan 1.4 a rana,wanda zai sanya a cinma burin Matatar Man ta zamo mafi girma a duniya a shekarar 2028. Sannan kuma Kamfanin na Honeywell zai samar da wasu na’urori na musamman wadanda za su sanya…
Karin Maganarmu Na Yau: Yau da gobe, mai sa a mari Amarya.
Kanfanin Dangote Ya Hada Gwiwa Da Abokan Huddarsa Don Bunkasa Noma Daga Abdullahi Yusuf Shahararren kanfanin nan na Dangote Group ya hada gwiwa da abokan huddarsa domin bunkasa harkokin noma a Nigeria. Wata sanarwa wadda mai magana da yawun kanfanin,Anthony Chiejina, ya sanya wa hannu, tace wannan yunkuri ya zo ne daidai lokacin da kanfanin ya dauki nauyin Bikin Nuna Fasahar Noma Na Kasa, karo na sha bakwai, wanda a ke farawa a birnin Keffi da ke cikin Jihar Nasarawa, a yau Talata,25 ga watan Nuwamba. Chiejina ya ce bunkasa aikin noma ta hanyar amfani da na’urorin zamani zai bunkasa…
Karin Maganarmu Na Yau: Amarya ba ta laifi,ko da ta kashe Dan Autan gida.
Karin Maganarmu Na Yau: Akwai yadda a ka yi, wai Maigida ya gode wa Kwarto.
Karin Maganarmu Na Yau: Allah, Allah, Amin,in ji Gardi ya so aure.
Karin Maganarmu Na Yau: Amarya ba ta laifi,ko da ta kashe Dan Autan gidan.
2027:”Yan Majalisar Dokokin Jihar Kano Na APC Sabbi Da Tsaffi Sun Fara Ziyarce-Ziyarce Don Hadin Kan “Yan Jam’iyya Daga Abdullahi Yusuf Kungiyar “Yan Majalisar Dokokin Jihar Kano na APC na da, da na yanzu, ta fara kai ziyarar ban girma ga gaggan Jam’iyyar da ke zaune a birnin tarayya, Abuja,a wani yunkuri na hada kan “Yan Jam’iyyar. Wannan Labari ya na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugaban Kungiyar,kuma tsohon Kakakin Majalisar,Alhaji AbdulAziz Garba Gafasa,ya rabawa “Yan Jarida a Kano,ranar Juma’ar nan. Gafasa ya ce,tuni Kungiyar ta kai ziyarar ban girma ga jagoran APC na Jihar Kano,tsohon Gwamnan Jihar…
2027:Dungurawa Ya Ce APC Na Bukatar Kwankwaso Don Ta Ci Zabe Daga Abdullahi Yusuf Shugaban Jam’iyyar NNPP reshen Jihar Kano,Alhaji Hashimu Suleiman Dungurawa,ya ce Jam’iyyar APC ta na bukatar Shugaban Kwankwasiyya na duniya baki daya,Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, domin ta ci zaben Shugaban Kasa na shekarar 2027. Dungurawa ya ce hakan ya kasance ne kuwa, saboda babu wani Dan Siyasa Mai goyon bayan “Yan Nigeria kamar Sanata Rabiu Kwankwaso. Ya yi wannan ikirari ne kuwa yayin da ya ke ganawa da manema labarai a cikin Ofishinsa ranan Al’hamis din da ta wuce. “A halin da a ke ciki, Jam’iyyar APC…