Ana bikin Ranar Hausa ta Duniya a ranar 26 ga Agusta na kowace shekara, domin tunawa da muhimmancin harshen Hausa da kuma al’adun Hausawa.
Daga Zainab Kamal Ibrahim
Bikin, wanda aka fara gudanarwa a shekarar 2015, ya samo asali ne daga ƙoƙarin masu ruwa da tsaki wajen amfani da kafafen sada zumunta wajen bunƙasa harshen Hausa da yaɗa shi zuwa sassa daban-daban na duniya.
Ranar Hausa ta Duniya na kuma zama wata dama ta haɗa masu magana da harshen tare da ƙarfafa ƙoƙarin kare shi daga tasirin sauye-sauyen zamani da kuma tabbatar da ci gaba da amfani da shi a fannoni daban-daban.
Adamu Ladan Ya Gina Makaranta Don Tallafa Wa Ilimi A Dandume
A bikin na bana, ana ƙara jaddada muhimmancin amfani da kimiyya da fasaha wajen bunƙasa harshen Hausa, musamman ta hanyar samar da abubuwan cikin Hausa a kafafen intanet da sauran sabbin hanyoyin sadarwa.
Hausa na daga cikin manyan harsunan da ake magana da su a Afirka, musamman a ƙasashen Yammacin Afirka, inda Najeriya ke da dimbin masu amfani da harshen.
Masana sun ce bunƙasar harshen na buƙatar ƙarin saka jari wajen bincike, koyarwa da samar da kayan ilimi da fasaha cikin Hausa, domin tabbatar da dacewarsa da buƙatun zamani.
Bikin Ranar Hausa ta Duniya na ci gaba da zama wata dama ta nuna alfahari da harshen Hausa da al’adun Hausawa, tare da ƙarfafa ƙoƙarin ganin harshen ya samu ƙarin karɓuwa a duniya.
