Author: Kabiru Basiru Fulatan

Nasiru Gawuna, jigo a jam’iyyar APC a Kano kuma Shugaban hukumar FMBN, ya ajiye mukaminsa. Gawuna ya ce murabus ɗin nasa ya fara aiki nan take, kuma ya yi dai-dai da umarnin shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na cewa duk masu riƙe da mukaman siyasa su sauka gabanin wasu harkokin siyasa. Shugaban NUJ Ya Yaba Da Aikin Kano Correspondents’ Chapel, Ya Kira ‘Yan Jarida Su Kara Hadin Kai Ya godewa shugaban Ƙasa bisa damar da aka ba shi na yin aiki, inda ya bayyana cewa hakan wata babbar dama ce. Rahotanni sun kuma nuna cewa Gawuna na shirin sauya sheƙa…

Read More

Shugaban ƙasa na Alhassan Yahya, ya yaba wa shugabannin ƙungiyar Kano Correspondents’ Chapel, NUJ saboda kafa ginshikin da ke karfafa kauna, hadin kai, da ci gaba a tsakanin ‘yan jarida a jihar Kano. Kwamared Yahya ya bayyana wannan ne a Cibiyar ‘Yan Jarida ta Kano a ranar Lahadi, a yayin taron walimar cin abinci da godiya ga Allah da ‘yan jaridar suka shirya bayan kammala Ibadar Azumin watan Ramadhana da kuma bukin Sallah. Sheikh Pantami Ya Roƙi El-Rufai, Ribadu Da Uba Sani Su Sulhunta A Jana’izar Mahaifiyarsa A jawabin sa, Shugaban NUJ ya bukaci mambobin kungiyar su ci gaba da…

Read More

Sheikh Dr. Isa Pantami ya buƙaci Malam Nasir El-Rufai da abokan siyasarsa su ajiye saɓanin da ke tsakaninsu, ya yi wannan kiran ne a makabarta yayin binne mahaifiyar El-Rufai, Hajiya Umma, a Abuja. Pantami ya yi wannan kira ne a huɗubarsa a maƙabartar Gudu ranar Lahadi. Ya roƙi shugabanni su fifita haɗin kai tare da tunawa da alherin da suka yi wa juna. Ya jaddada cewa rayuwa mai wucewa ce kuma dole kowa ya bar duniya wata rana. Ya ƙara da cewa nasara na zuwa ne ta bin hanyar Allah ba dabarun siyasa ba. A wurin jana’izar, manyan ‘yan siyasa…

Read More

Tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP nan take. Kwankwaso, wanda ya kasance jagoran jam’iyyar na kasa kuma dan takararta a zaben shugaban kasa na 2023, ya bayyana cewa ya dauki matakin ne bayan nazari kan yanayin siyasar kasar, domin samun wata sabuwar hanya da za ta ba shi damar kawo sauyi mai ma’ana. WAEC: Ɗalibai Sama da 10,000 Sun Rubuta Jarabawa, Kashi 32% Sun Samu Credits Biyar Ya gode wa shugabannin jam’iyyar, ciki har da shugaban jam’iyyar, Ajuji Ahmed, da sauran mambobin kwamitin gudanarwa na kasa, bisa goyon bayan da suka…

Read More

A sanarwar da mukaddashin shugaban hulɗa da jama’a na hukumar, Moyosola F. Adesina ya fitar daga hedikwatar WAEC da ke Yaba, ya ce an gudanar da jarabawar ne a cibiyoyi 166 a faɗin Najeriya daga 28 ga Janairu zuwa 14 ga Fabrairu 2026. Jimillar ɗalibai 10,480 ne suka rubuta jarabawar, daga ciki dalibai 3,429 kashi 32.72% sun samu credit a akalla darussa biyar ciki har da Turanci da Lissafi. An rantsar da Ali Musa Hardwoker a matsayin halartaccen shugaban karamar hukumar Kumbotso a Kano Wannan ya nuna ƙaruwa da kashi 5.76% idan aka kwatanta da sakamakon shekarar 2025 wanda ya…

Read More

Hukumar Zabe ta jihar Kano KANSIEC ta rantsar da Honarabul. Ali Musa Ɗanmaliki, (Hardwoker) a matsayin halartaccen shugaban karamar hukumar Kumbotso a Kano. Hukumar ta rantsar da Hardwoker, ne a yau Talata, bayan sauke Abdullahi Ghali Basaf daga shugaban karamar hukumar Kumbotso, yayin da aka maye gurbin sa da Ali Musa. Matatar Ɗangote ta fitar da tan 456,000 na man fetur zuwa wasu ƙasashen Afrika Bayan hukuncin babbar kotun jihar Kano na sauke Ghali Abdullahi Basaf daga shugabancin ƙaramar hukumar Kumbotso, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano ta mika shedar lashe zaɓe ga Hon. Ali Musa Hardworker. Shugaban…

Read More

Mamatar mai ta Ɗangote ta sanar da fara fitar da tataccen man fetur zuwa wasu ƙasashen Afrika, matakin da ke zuwa bayan da tayi iƙirarin wadata kasuwar cikin gida a Najeriya, duk da tsadar da yake yi a gidajen mai. Bayanai sun ce an fitar da manyan jiragen dakon man fetur guda 12 ɗauke da tan dubu 450 zuwa wasu ƙasashen Afrika biyar waɗanda rikicin gabas ta tsakiya ya fi yiwa fannin makamashinsu illa. Jami’an Hisbah Sun Kama Matasa Kusan 300 Da Suka Yi Askin Banza Da Kuma Kitso A Kano  Kafafen yaɗa labarai na cikin gida a Najeriya sun…

Read More

Hukumar Hisbah a jihar Kano ta kama matasa sama da 250 kan yin askin banza ko kuma kitse gashinsu. Mataimakin babban kwamandan hukumar, Mujahid Aminudden ne ya bayyana haka a bayanin da ya fitar game da ayyukan rundunar a bikin karamar Sallah. Ya ce daga cikin matasan akwai matuka Adaidaita Sahu da ke daukan mata a gefen baburansu. Gabanin bikin Sallar dai, hukumar ta fitar da sanarwar gargadi musamman ga matasa, kan kiyaye ayyukan da suka saba da tanadin addini da al’adun mutanen Kano.

Read More

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya taya al’ummar Musulmi murnar bikin ƙaramar Sallah, tare da kira gare su da su ƙara ƙaimi wajen nuna kishin ƙasa da kuma ƙarfafa haɗin kai a tsakanin al’umma. ‎A wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Alhamis, shugaban ya jaddada muhimmancin ci gaba da riƙe darussan da aka koya a watan Ramadan. ‎Ya ce darussa irin su tsoron Allah, haƙuri, tausayi da sadaukarwa na da muhimmanci wajen gina al’umma mai zaman lafiya, yana mai kira ga Musulmi da su ci gaba da amfani…

Read More

‎ Jam’iyyar Labour Party ta bayyana cewa za ta gudanar da Zaben fitar Gwani na  shugaban ƙasa na cikin gida ranar 23 ga Mayu, 2026, a matsayin shiri na tunkarar babban zaɓen 2027. ‎A lokaci guda, jam’iyyar ta dakatar da membobi 25 saboda zargin aikata abubuwa marasa kyau da suka saba wa ka’idojin jam’iyya. ‎Hukuncin ya fito ne daga taron Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) da aka gudanar a ranar Talata, inda Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanya ido. ‎Jam’iyyar ta ce za a miƙa jerin sunayen mambobi ga INEC ranar 15 ga Afrilu, 2026, yayin…

Read More