Daga Kwamared Abbas Ibrahim A shekara 27, Mikhail Kalashnikov ya kirkiri abin da daga baya ya zama daya daga cikin shahararrun bindigogin yaki a tarihin zamani, wato AK-47. A matsayinsa na soja kuma injiniya dan kasar Tarayyar Soviet a lokacin, Kalashnikov ya kirkiro makamin ne a lokacin Yakin Duniya na Biyu domin kare kasarsa daga mamaya. Bisa tarihin da aka sani, manufarsa ita ce kare kasa, ba yada hallaka a duniya ba. Abin da ya bambanta AK-47 shi ne saukin amfani da ita, juriyarta da kuma yadda ake iya sarrafa ta cikin sauki. Bindigar na aiki ko da a cikin…
Author: Abbas Ibrahim
A wani mataki na ƙarfafa tsarin darajar noma da inganta tsaron abinci a Najeriya, kamfanin BH Startup General Enterprise ya shiga haɗin gwiwa da FasterCapital a ƙarƙashin shirin su na Equity Pilot Program. Wannan haɗin gwiwar, wadda ta fara a watan Disamba 2025 a Kano, za ta taimaka wajen faɗaɗa aikin sarrafa shinkafa mara duwatsu na BH Startup tare da bunƙasa rarraba babbar hajarsu, wato BH Local Gold Rice, a yankunan Arewa da Arewa ta Tsakiya na Najeriya. Ta hanyar haɗa ƙwarewar FasterCapital a fannin bunƙasa sabbin kamfanoni da kuma tsarin sarrafa shinkafa na cikin gida na BH Startup, an…
Barka da Sallah! 🎉✨ Allah ya maimaita mana da alkhairi. Ga wasu Do’s (Abubuwan da ya kamata a yi) da Don’ts (Abubuwan da ya kamata a guje musu) a lokacin Sallah: ✅ DO’s – Abubuwan da ya kamata a yi Yin Sallar Idi da wuri a masallaci ko filin Idi Sanya tufafi masu tsafta da kyau (ba lallai sai sabo ba) Yin sada zumunci – ziyartar ‘yan uwa da abokai Yafiya da yafewa – gyara dangantaka da mutane Yin sadaqa/Zakatul Fitr (idan ba a yi ba kafin sallah) Yawan ambaton Allah (Takbiri: Allahu Akbar, Allahu Akbar…) Ciyar da marasa galihu…
Kamfanin Maltina ya bayyana cewa zai samar da ayyukan yi ga manoma sama da 20,000 a Jihar Jigawa nan da shekarar 2030, a wani sabon shiri da kamfanin ya ƙaddamar domin bunƙasa noman sha’ir (barley) da kuma ƙarfafa tattalin arzikin al’umma. Shirin, wanda aka gabatar da taken “Scaling Local Barley and Empowering Communities,” na da nufin tallafa wa manoma su rungumi noman zamani, tare da rage dogaro da shigo da irin sha’ir daga ƙasashen waje. Daraktan sashen Supply Chain na kamfanin, Federico Agressi, ya ce kamfanin ya ƙaddamar da shirin ne domin ƙarfafa manoma su koma yin noman…
A birnin Dubai na cikin Hadaddiyar Daular Larabawa, an sake ɗaga hankalin duniya bayan bayyanar wani katafaren ɗakin masauki da ya shiga sahun mafi tsada a doron ƙasa. Ɗakin da ake kira Royal Mansion, wanda ke cikin shahararren otal na Atlantis The Royal, na karɓar kuɗin kwana guda da ya kai kusan Naira miliyan 130, lamarin da ya mayar da shi ɗaya daga cikin wuraren kwana mafi alfarma a duniya. Masauki irin na sarauta a sararin sama Royal Mansion na da faɗin sama da murabba’in kafa dubu 11, tare da benaye biyu da dakunan…
Birnin Kano dake arewacin Najeriya ya haskaka da fitilu na musamman domin maraba da watan Ramadan, bayan da kamfanin Maltina ya kaddamar da wani sabon shiri mai suna Ramadan Light-Up. An gudanar da bikin kaddamarwar ne a harabar Emir Palace da ke Kofar Nassarawa, inda jami’an gwamnati da shugabannin al’umma da mazauna birnin suka halarta. Federico agressi “Daraktan Fasaha” ya ce shirya shirin manufarsa ita ce nuna muhimmancin watan Ramadan a matsayin lokaci na ibada, tunani, da haɗin kai tsakanin al’umma, musamman ta hanyar lokutan buɗe baki tare. Sun kuma bayyana cewa fitilun da aka kunna za su ci…
Wata Babbar Kotun Kano ts soke belin da aka bai wa Kabiru Aminu a shari’ar da ta shafi duka a unguwar Danladi Nasidi, Karamar Hukumar Kumbotso. An yanke hukuncin ne a Babbar Kotun Jiha ta 10 da ke Bompai Road, Kano, a gaban Mai Shari’a Aisha Yau, inda kotu ta amince da bukatar masu kara na soke belin bisa girman laifukan da ake tuhuma. Ana tuhumar Kabiru Aminu da shiga harabar wani ba bisa ka’ida ba, fashi da makami da yiwa Hajiya Rabi dukka da yankarta daya haddasa raunuka. Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta ce za…
Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti, ya sanya hannu kan Dokar Kula da Tsoffi wadda ke ba da gata na musamman ga duk ɗan asalin jihar da ya kai shekara 60 zuwa sama. Sabuwar dokar ta tanadi Albashi na wata-wata kyauta Jinya kyauta a asibitoci Sauran alawus-alawus da tallafi har zuwa rasuwa An ce manufar dokar ita ce rage raɗaɗin rayuwa ga tsofaffi, da tabbatar da walwalarsu, da kuma basu kariya ta zamantakewa bayan ritaya ko rashin ƙarfi. Masu sharhi na ganin matakin zai iya zama abin koyi ga sauran jihohi idan aka aiwatar da shi yadda ya kamata, tare…
Wani mummunan lamari ya faru a garin Keffi, Jihar Nasarawa, inda jama’a suka kashe tare da ƙone gawar wani tsohon dogari a Fadar Sarkin Keffi, da ake zargi da ƙwaƙule idanun wani yaro. An gano gawar yaron ne a cikin rami a wani gida a makwabtansu, lamarin da ya tayar da hankalin al’umma. ’Yan banga sun kama wanda ake zargin, amma jama’a suka mamaye su suka yi masa duka har lahira, suka kuma banka wa gawarsa wuta. ’Yan sanda sun isa wurin, amma ƙoƙarinsu na shawo kan jama’a ya gamu da turjiya, inda wasu jami’an suka…
Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano ta gana da shugabannin manyan kasuwannin jihar, domin tattauna hanyoyin da za su taimaka wajen rage tsadar kayan masarufi a yayin watan azumin Ramadan. Taron ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin shugaban hukumar, Kwamared Sa’idu Yahaya, inda aka haɗa shugabannin kasuwannin Singer, Sabon Gari, Na’ibawa ’Yan Lemo, Dawanau, da Kasuwar Turawa ta ’Yan Kaba. Da yake jawabi a wajen taron, Kwamared Sa’idu Yahaya ya ce an kira ganawar ne domin samun fahimta da haɗin kai da ’yan kasuwa, ta yadda za a sauƙaƙa wa jama’a samun kayan abinci…