Wani mummunan lamari ya faru a garin Keffi, Jihar Nasarawa, inda jama’a suka kashe tare da ƙone gawar wani tsohon dogari a Fadar Sarkin Keffi, da ake zargi da ƙwaƙule idanun wani yaro.
An gano gawar yaron ne a cikin rami a wani gida a makwabtansu, lamarin da ya tayar da hankalin al’umma.
’Yan banga sun kama wanda ake zargin, amma jama’a suka mamaye su suka yi masa duka har lahira, suka kuma banka wa gawarsa wuta.
’Yan sanda sun isa wurin, amma ƙoƙarinsu na shawo kan jama’a ya gamu da turjiya, inda wasu jami’an suka jikkata.
Mahaifin yaron, Muhammadu Lawal, ya bayyana cewa ya taɓa samun saɓani da wanda ake zargin kan hayaniya da ya riƙa yi da dare.
Ya ce, “Na taɓa samun matsala da wannan mutumin saboda hayaniyar da yake yi da dare. Na gan shi da kyandir da ƙwarya da kuma ’yar tsana a gabansa. Na bar wa Allah komai, Shi Kaɗai Ya san ko wannan kisan yana da alaƙa da saɓaninmu da shi kwanaki kaɗan da suka gabata.” kamar yanda Jaridar AMINIYA ta ruwaito
Malam Lawal ya ce ya gano gawar ɗansa a cikin rami, an ƙwaƙule masa idanu, aka yanke masa wuya, kuma aka yi masa rauni da wuƙa.
Yahaya Ladan Shafale, mai rike da sarautar Kakakin Sarkin Keffi, ya tabbatar wa wakinmu cewa an riga an sallami wanda ake zargin daga fadar tun kafin faruwar lamarin.
“Tun da daɗewa Sarkin ya sallame shi daga aiki. Bayan sallamarsa ne muka ji labarin ya kashe yaro a unguwa.”
Shafale ya bayyana kisan a matsayin abin “ban mamaki” da “ban tsoro,” yana mai cewa: “Keffi gari ne mai tarihi da albarka, ba za mu taɓa so irin wannan lamari ya sake faruwa ba.”
Kakakin ’yan sanda na jihar, SP Ramhan Nansel, ya tabbatar da faruwar lamarin da misalin ƙarfe 12:30 na rana.
Ya ce sun samu kiran gaggawa daga Dogara Garba, ’yan banga na Sabon Kasuwa, cewa sun kama wanda ake zargi. Sai dai kafin ’yan sanda su isa, jama’a sun mamaye ofishin, suka kashe wanda ake zargin, sannan suka ƙone gawarsa.
“Kafin mu isa, an riga an kashe shi kuma an ƙone gawarsa. Jama’a ma sun kai wa ’yan sanda hari, suka jikkata wasu jami’an tare da lalata motocinsu.
“Daga baya ’yan sanda sun shawo kan lamarin, suka ɗauke gawar zuwa Babban Asibitin Gwamnati na Keffi, inda bincike ya ke ci gaba,” in ji shi.
Lamarin ya tayar da hankalin jama’a, inda ake kira da a tabbatar da adalci.
