Author: Abbas Ibrahim

An kammala taron kwana huɗu da asusu majalisar dinkin duniya (UNFPA) ta shirya a hotel din Tahir dake garin kano, kan inganta kyawawan halayen maza, inda mahalarta suka ƙirƙiro tsare-tsare na ayyuka domin magance aurar da ƙananan yara, kaciya ga mata (FGM), da kuma cin zarafin jima’i da na jinsi (SGBV). Mahalarta taron, waɗanda suka fito daga kungiyoyin matasa da na al’umma daban-daban, ana sa ran za su fara aiwatar da ayyukan da aka tsara kafin 31 ga watan Disambar shekarar ta 2025. Da take jawabi a Yayin rufe taron, jami’ar UNFPA Hajiya Bahijja Bello Garko ta tabbatar da kudirin…

Read More

Kimanin Mata da kuma Yara Mata Miliyan 68 a ƙasarnan ne suka fuskanci cin zarafi ta hanyar yi musu Kachiya wanda yake nuni da cewa kimanin kaso 22 cikin Ɗari na Mata Miliyan 230 da aka yiwa Shayi a Duniya sun fito ne daga Najeriya kamar yadda aka bayyana a wani taron Bitar wayar da kai kan illlar yiwa Mata Kachiya da aka gudanar a nan birnin Kano. A yayin da take magana a rana 3 ta taron Bitar wanda yake gudana a Otel din Tahir, wata Mai rajin kare haƙƙin Mata mai suna Hajiya Karima Bungudu ta bayyana cewa…

Read More

Yau Talata ta kasance kwanaki takwas , da rasuwar mamallakin shagunan siyar da maganguna na Lamco Alhaji Ado Aminu Mai Sh inkafa wanda aka fi sani da Alhaji Ado Lamco, Daya daga cikin manajojinsa, Malam Abdullahi Idris ya bayyana dalilin da yasa aka cigaba da siyar da magunguna a shagunan duk da rasuwar mai shagunan. Da yake Jawabi a masallacin da Alhaji Ado Lamco ya gina, bayan rasuwarsa, Malam Abudullahi Idris yace tun lokacin marigayin yana raye ya bayar da wasiyya cewa ko bayan ya rasu a cigaba da siyarwa al’umma magunguna a shagunan. Yace marigayin ya jaddada cewa ko…

Read More

Daga Mustapha Muhammad Yawaitar Al’ummar Jihar Kano dake Arewa maso Yammacin Najeriya cikin hanzari, ta kasance wani babban abin damuwa, musamman a ƙoƙarin samar da isasshen abinci da aikin yi da tallafawa matasa da mata. Hakan ce ta sa karfafa wa manoma gwiwa domin noma ƙarin hatsi da nau’in tsirrai masu yaɗo, har ma da fito da hanyoyin daga darajar amfanin gona yake da matukar muhimmanci. Saboda haka ne Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya tsaya kai da fata wajen sauya fasalin harkar noma a fannoni uku: haɓaka samar da amfanin gona, sarrafawa da kuma kasuwanci. A…

Read More

Shahararren Wanzami, Alhaji Musa Kawu Wanzami, ya bayyana rasuwar ɗan kasuwar Kano, Alhaji Ado Aminu (Mai Shinkafa), wanda aka fi sani da Alhaji Ado Lamco, a matsayin babban rashi da ya bar gibi mai wahalar cikewa. Alhaji Musa Wanzami, wanda ke gudanar da harkokinsa kusa da Lamco Pharmacy da ke kusa da Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH), ya ce ya shafe fiye da shekaru 20 yana tare da marigayin. Ya bayyana Alhaji Ado a matsayin mutum mai karamci, sauƙin kai da tausayi, wanda ya taɓa rayuwar mutane da dama ta hanyar ayyukan alheri. A cewarsa, Alhaji Ado Lamco…

Read More

Daruruwan Jama,a sun yi tururuwa a fadar Mai Martaba Sarkin Kano da yammacin Asabar domin halartar jana’izar Alhaji Ado Aminu Mai Shinkafa, da aka fi sani da Alhaji Ado Lamco. An gudanar da sallar jana’izar ne bayan sallar La’asar, karkashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II. Daga nan dandazon jama’a suka raka gawar zuwa Makabartar Ado Dandolo, inda aka yi masa sutura. Alhaji Ado Lamco fitaccen ɗan kasuwa ne a bangaren magunguna da kiwon lafiya, kuma shi ne ya kafa kantin magunguna Lamco Pharmacy, Wanda ya shahara a fadin Kano. Ya rasu ne a ranar…

Read More

Daga Abba Anwar Gungun wasu kwararru kan nazarin sammatsin siyasa da ci gaban ta sun gudanar da wani bincike kan wasu jagororin ‘yan siyasa daga arewacin Najeriya. An yi wannan bincike ne kan dukkanin jihohin arewa 19. A binciken nasu daga cikin wadanda su ka gama tattara bayanai sun hada da jihar Kano da wasu kalilan daga jihohin arewan. A jihar Kano sai su ka zakulo mataimakin shugaban Majalisar Dattawa na Kasa, wato Sanata Barau Jibrin da yake wakiltar Kano Ta Arewa. Da kuma dan majalisar tarayya mai wakiltar Tudunwada-Doguwa, a majalisar wakilai ta kasa, wato Alhassan Ado Doguwa.…

Read More

Danga Kwamared Abbas Ibrahim Na daɗe ina son yin wannan rubutu amma ban yi ba, ba wai saboda wani takunkumin doka ba. Domin kuwa sashi na 39 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya ba da ‘yancin fadin albarkacin baki. Sai dai a halin yanzu ne na ga dacewar lokacin yin wannan rubutu. Yanzu da na yi ritaya daga aiki a ranar 1 ga Nuwamba, 2025, bayan ajiye aiki a matsayin Editan Labarai a gidan Radio Kano dake zama cibiyar gwamnati da ake alfahari da ita wadda kuma za ta cika shekaru 80 da kafuwa a shekara mai zuwa — na…

Read More

Aikin Wucin Gadi: Babban Barazana Ga Ci Gaban Dan Adam Dsga Comrade Abbas Ibrahim Aikin wucin gadi ya zama babban kalubale ga ci gaban dan adam, yayin da miliyoyin ma’aikata ke tsaka da ayyuka marasa tabbaci, marasa kyau, da rashin kariya. Masana aiki na gargadin cewa wannan dabi’a, wadda ta yadu a fannoni da dama, na rage yawan aiki mai inganci, da kwanciyar hankali a cikin al’umma, da kuma ci gaban kasa a dogon lokaci. Ma’aikatan wucin gadi sau da yawa suna samun albashi kasa da na ma’aikatan dindindin, ba sa samun wasu hakkoki kamar fansho ko inshorar lafiya, sannan…

Read More