DAGA ZAINAB KAMAL IBRAHIM
Hukumar yaƙi da safarar mutane a Najeriya NAPTIP ta kuɓutar da mutum 15 har da baƙi bayan da ta bankaɗo wata ƙungiyar masu safarar mutane da ake zargi tana aiki a matsayin kamfanin tallata kayayyaki ta intanet a jihar Nasarawa.
NAPTIP ta kuɓutar da mutanen ne bayan samamen da jami’anta suka kai ƙananan hukumomin Karu da Keffi sakamakon sahihan bayanan da suka samu a kan kamfanin.
Najeriya Za Ta Kashe Dala Biliyan 11.6 Wajen Biyan Kudin Ruwan Basussuka A 2026 — Shugaba Tinubu
NAPTIP ta sanar da haka ne cikin sanarwar da ta wallafa a shafinta na X ranar Laraba.
Ta ce an kai samamen ne a ranar 7 ga watan Mayu inda ta ce cikin mutanen da aka kuɓutar akwai mata huɗu da maza 11. Cikin mazan, uku ƴan Najeriya ne sai sauran da suka fito daga wasu ƙasashen.
