DAGA ZAINAB KAMAL IBRAHIM
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta kashe kimanin dala biliyan 11.6 wajen biyan kuɗaɗen ruwa da sauran basussukan da ake bin Najeriya a shekarar 2026.
Tinubu ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin jawabi a taron Africa Forward Summit da aka gudanar a cibiyar taruka ta Kenyatta International Convention Centre da ke birnin Nairobi.
Rikicin ACF: Lokaci Ya Yi Na Rushe Tsohon Tsari Da Yin Garambawul —Abbas Ibrahim
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar, shugaban ya ce kuɗin da za a kashe wajen biyan bashin ya kai kusan rabin abin da gwamnatin tarayya ke sa ran samu a matsayin kuɗaɗen shiga a shekarar.
Tinubu ya nuna damuwa kan yadda tsadar kuɗin ruwa da ƙasashen Afirka ke biya wajen karɓar lamuni ke kawo tsaiko ga bunƙasar masana’antu da ci gaban tattalin arzikin nahiyar.
“Duk wata dala da ke fita daga baitul malinmu domin biyan tsadar ruwa, dala ce da ba a saka ta wajen bunƙasa masana’antar ƙarafa, masaku, sarrafa kayan noma ko masana’antun fasahar zamani ba,” in ji shugaban.
Ya ƙara da cewa irin wannan yanayi na rage damar horas da matasa masu ƙwarewa a fannin injiniya tare da kawo cikas ga samar da wutar lantarki mai araha domin bunƙasa masana’antu.
Shugaban ya kuma bayyana cewa duk da ƙoƙarin da Najeriya ke yi wajen gyaran tsarin kuɗinta, cibiyoyin bayar da lamuni da hukumomin ƙididdigar kuɗi na duniya na ci gaba da kallon ƙasashen Afirka a matsayin masu haɗarin bashi.
A cewarsa, hakan ne ke sa ƙasashen nahiyar ke karɓar lamuni da tsadar ruwa mai yawa idan aka kwatanta da ƙasashen Turai, Asiya da Arewacin Amurka.
Tinubu ya ce wannan matsala na kawo cikas ga burin ƙarfafa haɗin gwiwar masana’antu tsakanin ƙasashen Afirka ƙarƙashin yarjejeniyar cinikayya ta bai ɗaya ta nahiyar Afirka, wato African Continental Free Trade Area.
Sai dai shugaban ya ce gwamnatin sa ta samu nasarar farfaɗo da ɓangaren bankunan Najeriya, inda ya bayyana cewa jarin bankunan ƙasar yanzu ya haura dala biliyan 3.4.
Ya ƙara da cewa hakan ya taimaka wajen cire Najeriya daga jerin ƙasashen da Financial Action Task Force ke sanya ido a kansu kan matsalolin hada-hadar kuɗi da safarar kuɗaɗe ba bisa ƙa’ida ba..
