Mamatar mai ta Ɗangote ta sanar da fara fitar da tataccen man fetur zuwa wasu ƙasashen Afrika, matakin da ke zuwa bayan da tayi iƙirarin wadata kasuwar cikin gida a Najeriya, duk da tsadar da yake yi a gidajen mai.
Bayanai sun ce an fitar da manyan jiragen dakon man fetur guda 12 ɗauke da tan dubu 450 zuwa wasu ƙasashen Afrika biyar waɗanda rikicin gabas ta tsakiya ya fi yiwa fannin makamashinsu illa.
Jami’an Hisbah Sun Kama Matasa Kusan 300 Da Suka Yi Askin Banza Da Kuma Kitso A Kano
Kafafen yaɗa labarai na cikin gida a Najeriya sun ruwaito cewa tuni aka kammala sayar da man fetur ɗin, abinda ke alamta cewa ƙasashen na tsananin buƙatarsa.
Ƙasashen da aka shigarwa da man Fetur ɗin daga Najeriya sun haɗar da Côte d’Ivoire, Kamaru, Tanzania, Ghana, da kuma Togo, abinda ke nuna irin bunƙasar da matatar ta samu tun bayan kafata.
Guda daga cikin manyan jami’ai a matatar da ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce wannan ya nuna irin buwayar da Najeriya ke da ita a fannin makamashi da kuma ƙarfin kasuwa.
Tan dubu 456 na man fetur ɗin da aka fitar dai-dai yake da lita miliyan 608, abinda babu shakka zai bunƙasa ƙarfin masana’antar da kuma haɓɓaka cinikin da ake samu a kowacce rana..
