Kamfanin Maltina ya bayyana cewa zai samar da ayyukan yi ga manoma sama da 20,000 a Jihar Jigawa nan da shekarar 2030, a wani sabon shiri da kamfanin ya ƙaddamar domin bunƙasa noman sha’ir (barley) da kuma ƙarfafa tattalin arzikin al’umma.

Shirin, wanda aka gabatar da taken “Scaling Local Barley and Empowering Communities,” na da nufin tallafa wa manoma su rungumi noman zamani, tare da rage dogaro da shigo da irin sha’ir daga ƙasashen waje.


Daraktan sashen Supply Chain na kamfanin, Federico Agressi, ya ce kamfanin ya ƙaddamar da shirin ne domin ƙarfafa manoma su koma yin noman zamani wanda zai ƙara yawan amfanin gona da kuma bunƙasa tattalin arzikin al’ummomin karkara.

Ya ce a halin yanzu Najeriya na shigo da tan dubu 200 na sha’ir a kowace shekara, lamarin da ke sa a kashe kimanin dala miliyan 150 wajen shigo da irin daga ƙasashen waje.

A cewarsa, burin shirin shi ne a samar da wannan amfanin gona a cikin gida, ta yadda za a rage kuɗaɗen da ake kashewa wajen shigo da shi daga waje, tare da samar da ci gaba mai ɗorewa ga manoma.

A nasa jawabin, Manajan Daraktan kamfanin, Tibo Brochain, ya ce shirin yana daga cikin ƙoƙarin kamfanin na samar da ayyukan yi da kuma bunƙasa harkar noma a Najeriya.
Ya ce an fara aiwatar da shirin a jihohi da dama da suka haɗa da Bauchi, Kano, Plateau, Gombe, Yobe da Jigawa, domin tallafa wa manoma da kuma ƙarfafa samar d sha’ir a cikin gida.
Brochain ya kuma gode wa cibiyoyin bincike, kamfanoni masu zaman kansu da hukumomin gwamnati da suka ba da goyon baya wajen ganin shirin ya samu nasara.
Shi ma Dutel Ambassador, Bengt Van-L, ya ce shirin na da burin sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da za su zama kan gaba wajen noman sha’ir idan aka ci gaba da irin wannan haɗin gwiwa tsakanin manoma da kamfanoni masu zaman kansu.
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, wanda Kwamishinan Noma na jihar, Muttaka Namadi, ya wakilta, ya ce shirin babbar dama ce ga jihar da ta shahara wajen harkar noma.
Ya ce gwamnatin jihar na maraba da wannan shiri saboda zai taimaka wajen ƙara samar da ayyukan yi, bunƙasa tattalin arzikin manoma da kuma ƙara yawan amfanin gona.
Haka kuma ya yaba wa kamfanin Maltina kan wannan shiri, yana mai cewa manoma a jihar sun nuna farin ciki da yadda shirin zai ƙara musu hanyoyin samun kuɗaɗen shiga.
A nasa jawabin, Sarkin Ringim, Alhaji Sayyadi Abubakar Mahmoud (CON) wanda Madakin Ringim, Alhaji Bashir Sha’aibu, ya wakilta, ya yi kira ga manoma su ba kamfanin cikakken haɗin kai domin tabbatar da nasarar shirin.
Shi kuma Shugaban manoman Ringim, Dr. Mujitapha Ubaye, ya ce manoma sun shirya tsaf domin yin iya ƙoƙarinsu wajen samar da amfanin sha’ir fiye da yadda aka tsara.
Taron ƙaddamar da shirin ya samu halartar wakilan cibiyoyin binciken noma, hukumomin gwamnati da kuma manyan baƙi daga sassa daban-daban na Najeriya.
