A Jihar Kano da ke arewacin Najeriya, aƙalla mutane 10,000 masu cancantar kaɗa ƙuri’a ne suka yi rajistar katin zaɓe a wani babban shiri na kwanaki shida da aka gudanar a jihar.
Shirin, wanda aka tsara domin ƙarfafa rajistar masu jefa ƙuri’a, ya samu halartar jama’a da dama, lamarin da masu shirya shi suka ce ya nuna yadda al’umma ke ƙara fahimtar muhimmancin shiga harkokin dimokuraɗiyya.
Kano: Indabo Ta Haskaka Ayyukan Gwamnatin Abba Kabir Yusuf
Kwamitin da ke kula da shirin ya bayyana cewa sakamakon da aka samu ya zarce hasashen da aka yi tun farko, inda dubban matasa da sauran ‘yan ƙasa suka fito domin yin rajista.
Jami’an kwamitin sun kuma sanar da aniyarsu ta faɗaɗa wannan shiri zuwa ƙarin yankuna, musamman a karkara, domin bai wa mutane da dama damar yin rajista cikin sauƙi.
A cewar masu ruwa da tsaki, irin wannan yunƙuri na taimakawa wajen ƙara yawan masu jefa ƙuri’a tare da inganta sahihancin zaɓe a Najeriya.
Masu sharhi kan harkokin siyasa sun ce wannan mataki na iya ƙara wa tsarin dimokuraɗiyya ƙarfi, musamman idan aka ci gaba da wayar da kan jama’a kan muhimmancin kaɗa ƙuri’a.
Ana dai kallon wannan shiri a matsayin wani muhimmin mataki na shirye-shiryen zaɓukan da ke tafe a ƙasar.
