Daga Abba Anwar
Akwai tunani daga mutane da yawa kafin zabubbukan da a ka gudanar na shugabannin jam’iyyar APC a jihar Kano da a ka gudanar kwanakin baya cewar, da wuya Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya iya gudanar da zabubbukan cikin nasara.
Jama’a sun yi wannan tunanin ne ba wai dan shi Gwamnan bai jima da shigowa jam’iyyar ta APC ba ne. A’a an yi wannan tunani ne ta yin la’akari da irin rigingimun dake cike fal a jam’iyyar a jihar Kano. Ta gefe da gefe ta sama ta kasa, ta ko’ina ma.
Kano: Kotu ta umarci matashi ya biya kuɗin maganin wanda ya jikkata
Musamman kuma idan a ka kara yin la’akari da daga wajen da ya fito. Wajen da akwai tsarin shugabanci na bai daya, mai yin biyayya ga na sama. Wanda duk wata damuwa da rashin yarda a ke shanye su a ciki.
Kuma wani abin karfafa gwuiwa da ban sha’awa daga bangaren Gwamnan shine, yadda ya karbi tsarin rabon shugabancin tsakaninsa da tsoffin ‘yan APC da ya samu a ciki. Wato yadda a ka kasa tsarin shugabancin kan cewa shi zai dauki kashi 60 cikin dari. Yayin da su kuma za a ba su kashi 40 cikin dari.
Gwanin ban sha’awa da burgewa shine, yadda a wasu wuraren Gwamnan ya salwantar da nasa kason na kashi 60 ya ba ‘yan tsohuwar APC din da ya tarar, shi kuma ya tafi da kashi 40. Yin hakan da ya yi dan kashin kansa ya yayyafa ruwan sanyi kan dambarwar cikin gida da ta addabi APC din a tsahon lokaci. Ba mai iya wannan sai gwarzon shugaba.
Babban abin ban sha’awa kuma shine, yadda Gwamnan yai hobbasa wajen ganin an yi zabubbukan shugabannin jam’iyyar tun daga matakin mazaba zuwa kananan hukumomi har zuwa matakin jiha. An ma rasa wace hikima ko wane siddabaru ya yi wajen ganin duk zabubbukan an yi su bisa kwanciyar hankali. Illa iyaka kawai ‘yan wasu korafe-korafe da ba a rasa ba. Amma a gaba dayan zaben an yi ne bisa nasara da kwanciyar hankali.
Yadda a ka samu nasara a nan Kano ba kamar yadda a ka yi a wasu jihohin ba ne wadanda Gwamnoninsu su ka tsallaka zuwa APC, kafin zaben nan da yake tunkarowa na 2027. A wasu jihohin ma irin wannan, ai kusan a ce an samu shugabancin jam’iyyar na jiha guda biyu mabanbanta.
Shi Gwamnan Kano kamar yadda masu nazari ke fada, babbar sa’ar da ya samu ita ce, da ya shigo cikin APC sai ya samu goyon bayan dukkan bangarorin dake rashin jituwa da juna, su ka mara masa baya dan cigaban jam’iyyar.
Wani babban abin lura kuma shine, matsawar dai Gwamna zai fahimci muhimmancin samun goyon bayan masu fada a ji a APC din da ya tarar, to kuwa ya fara dauko hanyar samun nasarar mulkinsa da kuma samun nasarar jam’iyyar a zabe mai zuwa na 2027. A nan ina magana ne kan wasu jiga-jigai su biyu na APC din. Wato mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I Jibrin, CFR, da kuma Maigirma Murtala Sule Garo.
A zance na gaskiya ba na rufa-rufa ba, dole Gwamna ya na bukatar cikakken goyon bayan wadannan shugabanni. In har burin shine samun nasarar mulkinsa da kuma samun nasarar jam’iyyar a zabe mai zuwa. Ni a waje na, dukkansu babu kashin jefarwa.
Wani abu kuma da nake kalubalantar jama’a a kai shine, duk da yadda a ke yada cewar wai akwai mummunar gaba ta siyasa tsakanin wadannan manyan, har yanzu ba wanda zai ce mun ya gani ko ya san wata rana da Barau ya bayar da kudi ya ce a je a soki ko a ci mutuncin Garo a radio ko a wasu kafafe ba.
Haka nan ban ga wani wanda zai ce min ya gani ko ya ji ga wata rana da Garo ya bayar da kudi ya ce a je a shiga gidan radio ko a je wasu kafafe a soki ko a ci mutuncin Barau ba. Ni a waje na dukkan wadannan matsalolin ba su wuce na ‘yan kankajere da ‘yan gaza-gani ba. Amma fa wannan a nawa nazarin ne. Ban san ko da gyara ba.
Ga ita kuma uwar jam’iyyar APC ta kasa, ina ga ya kamata a ce sun yi wata jinjinawa ta musamman ga Gwamnan Kano, saboda yadda ya tsaya ya tabbatar an yi zaben shugabannin jam’iyya daga mazabu zuwa kananan hukumomi har zuwa matakin jiha. Ba tare da an yi batacciya a wajen zabukan ba. A nawa hangen wannan shine ainihin alamun shugabanci nagari. Ya kamata uwar jam’iyyar ta yi masa wannan jinjinawa lokacin babban zabe na kasa, ko ma kafin lokacin.
Shi fa nasa tsarin da yanayin samun nasararsa ya wuce, yadda da yawa daga cikin Gwamnonin da suka tsallako APC din su ka yi a lokacin zabubbukan shugabancin jam’iyyar a jihohinsu.
Misali kamar Gwamnonin jihohin Delta, Sheriff Oborevwori, da na Akwa, Ibom Umo Eno, da na Bayelsa, Duoye Diri, da na Rivers, Siminalayi Fubara, da na Plateau, Caleb Mutfwang, da na Taraba Agbu Kefas, da na Adamawa, Umaru Fintiri da kuma na Enugu, Peter Mbah. Zabubbukan jihar Kano da akwai saukin rikici da dambarwa kan na wadannan jihohin da na zayyana din nan.
Ina ganin ya kamata a kara karawa Gwamnan na Kano kwarin gwuiwa wajen yaba masa saboda wannan babban kokarin da ya yi. Wanda ba wanda ya yi tsammanin za a samu irin wannan nasara ganin yadda a ke ta hayaniya a cikin jam’iyyar ta APC tun ma kafin shigowar Gwamnan.
Abin mamaki a wasu jihohin fa sai da ta kai jallin an samu kusan shugabanci guda biyu na jam’iyyar a matakin jiha. Wanda a Kano kuma ba wannan maganar.
Anwar ya rubuto wannan daga Kano
Litinin, 16 ga watan Maris, 2026
