Ana zargin wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da wasu matafiya da ke cikin tawagar rakiyar amarya daga garin Sheme na Jihar Katsina zuwa Jihar Kebbi, lamarin da ya sake nuna ƙalubalen tsaro a hanyoyin Arewa maso Yamma.
Daga Zainab Kamal Ibrahim
Rahotannin sun ce lamarin ya fito ne ta bakin mai ba da rahotanni kan harkokin tsaro a yankin Arewa maso Yamma, Bakatsine, wanda ya wallafa a shafinsa na X cewa tawagar ta faɗa hannun ’yan bindiga ne yayin tafiyarsu zuwa Jihar Kebbi domin rakiyar amarya.
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
A cewarsa, an yi garkuwa da wasu daga cikin mutanen da ke cikin tawagar, inda ya yi kira ga al’umma da su yi addu’a domin samun kubutar waɗanda abin ya shafa cikin koshin lafiya.
Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a bayyana takamaiman wurin da harin ya faru ba, haka kuma ba a tabbatar da adadin mutanen da aka sace ba.
Kazalika, jami’an tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba, yayin da har yanzu ba a san halin da waɗanda aka yi garkuwa da su ke ciki ba.
