Wasu kansiloli biyu na Ƙaramar Hukumar Fagge da ke Jihar Kano sun zargi Shugaban Ƙaramar Hukumar, Alhaji Salisu Usman Masu, da hannu wajen shirya harin da wasu da ake zargin ’yan daba ne suka kai musu bayan wani taro da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya halarta.
Daga Zainab Kamal Ibrahim
Kansilan ’Yanmata Gabas, Shamsu Ali Umar, da Kansilan Fagge D1, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Ƙaramar Hukumar, Sani Muhammad, sun ce lamarin ya faru ne a harabar Asibitin Cutar Masu Yaɗuwa (IDH) bayan kammala taron da gwamnan ya halarta a ranar Litinin.
Aminiya ta ruwaito Cewa Sani Muhammad ya bayyana cewa, yayin da suke shirin komawa motocinsu, wasu mutane kimanin 30 ɗauke da makamai suka afka musu tare da yi musu duka.
Ya ce an buge shi da sanda a kai har ya samu rauni, yayin da wani kansilan ma ya ji rauni.
A cewarsa, jami’an tsaro ne suka shiga tsakani suka ceto shi, yayin da sauran kansilolin suka tsere domin kauce wa harin.
