Shugaban ƙasa na Alhassan Yahya, ya yaba wa shugabannin ƙungiyar Kano Correspondents’ Chapel, NUJ saboda kafa ginshikin da ke karfafa kauna, hadin kai, da ci gaba a tsakanin ‘yan jarida a jihar Kano.
Kwamared Yahya ya bayyana wannan ne a Cibiyar ‘Yan Jarida ta Kano a ranar Lahadi, a yayin taron walimar cin abinci da godiya ga Allah da ‘yan jaridar suka shirya bayan kammala Ibadar Azumin watan Ramadhana da kuma bukin Sallah.
Sheikh Pantami Ya Roƙi El-Rufai, Ribadu Da Uba Sani Su Sulhunta A Jana’izar Mahaifiyarsa
A jawabin sa, Shugaban NUJ ya bukaci mambobin kungiyar su ci gaba da amfani da darussan da suka koya a watan Ramadhana, musamman dabbaka hadin kai, zaman lafiya, da hakuri yayin gudanar da ayyukansu na yau da kullum.
Hakanan, Kwamared Yahya ya samu wakilcin tsohon shugaban NUJ reshen Kano kuma mamba a Kwamitin Amintattu na NUJ, Abbas Ibrahim, wanda ya bayyana cewa a karkashin jagorancin Murtala Adewale, an samu gagarumin ci gaba a cikin shekara guda, musamman a ayyukan da suka shafi al’umma.
Kwamared Ibrahim ya kara jaddada muhimmancin nuna kauna da hadin kai a tsakanin ‘yan jarida wajen fuskantar kalubale na samar da abinci, kiwon lafiya, da tsaron al’umma..
