Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya taya al’ummar Musulmi murnar bikin ƙaramar Sallah, tare da kira gare su da su ƙara ƙaimi wajen nuna kishin ƙasa da kuma ƙarfafa haɗin kai a tsakanin al’umma.
A wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Alhamis, shugaban ya jaddada muhimmancin ci gaba da riƙe darussan da aka koya a watan Ramadan.
Ya ce darussa irin su tsoron Allah, haƙuri, tausayi da sadaukarwa na da muhimmanci wajen gina al’umma mai zaman lafiya, yana mai kira ga Musulmi da su ci gaba da amfani da su a rayuwarsu ta yau da kullum.
Rahotanni daga Jaridar INDA RANKA sun ambato shugaban yana ƙarfafa gwiwar al’umma da su riƙa taimakon masu buƙata ba tare da la’akari da bambancin addini ko ƙabila ba.
Haka kuma, ya buƙaci shugabannin addini da su ƙara himma wajen yi wa ƙasar addu’o’in zaman lafiya da ci gaba.
Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnatin Najeriya za ta ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin inganta walwalar al’umma da samar da yanayi mai kyau ga ci gaban ƙasa.
