Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ), reshen Jihar Kano, ta bayyana alhininta kan rasuwar tsohon ɗan jarida kuma gogaggen mai gudanar da harkokin yaɗa labarai, Alhaji Adamu Ibrahim Getso.
A cikin wata sanarwa da sakatariyar ƙungiyar, Hauwa Suleiman Zahradeen, ta fitar a ranar Talata, shugaban NUJ na Kano mai riƙon ƙwarya, Mustapha Gambo, ya miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan marigayin, abokansa da kuma al’ummar Getso da ke Ƙaramar Hukumar Gwarzo.
Gwamnatin Kano Ta Dakatar Da Sare Bishiyoyi A ARTV, Ta Gano Matsalolin Gudanarwa
Ya ce rasuwar Adamu Getso babban rashi ne ga harkar aikin jarida da kuma al’ummar Kano, duba da irin gudunmawar da ya bayar tsawon shekaru a fannin yaɗa labarai.
“Marigayi Adamu Getso ƙwararren ɗan jarida ne wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa al’umma hidima ta hanyar yaɗa sahihan bayanai da wayar da kan jama’a. Gudunmawar da ya bayar za ta ci gaba da kasancewa abin tunawa a tarihin aikin jarida a Kano,” in ji Gambo.
Sanarwar ta bayyana cewa marigayin ya taka muhimmiyar rawa a matsayin babban mai gabatar da shirye-shiryen siyasa da ci gaba a lokacin mulkin tsohon gwamnan Kano, Dakta Rabiu Musa Kwankwaso, inda ya yi amfani da ƙwarewarsa wajen isar da bayanai da ilimantar da jama’a kan ayyukan gwamnati da al’amuran da suka shafi rayuwar yau da kullum.
NUJ ta ce marigayin ya kasance abin koyi ga matasa masu tasowa a harkar jarida saboda ƙwazonsa, ƙwarewarsa da jajircewarsa wajen gudanar da aiki cikin gaskiya da ƙwarewa.
Ƙungiyar ta yi addu’ar Allah Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya sanya shi a Aljannatul Firdaus, tare da bai wa iyalansa da daukacin al’ummar da ya bari haƙurin jure wannan babban rashi.
Rasuwar Adamu Ibrahim Getso ta jefa al’ummar kafafen yaɗa labarai a Kano cikin jimami, yayin da ake ci gaba da tuna irin gudunmawar da ya bayar wajen bunƙasa aikin jarida da wayar da kan jama’a.
