Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta sanar da ɗage aikin sabunta rajistar masu zaɓe da ta shirya yi a duk faɗin ƙasar nan zuwa bayan babban zaɓen shekarar 2027 kamar yadda jaridar The Nation ta rawaito.
An yanke wannan shawara ne bayan wani taro da hukumar ta gudanar da Kwamishinonin Zaɓe na jihohi, inda aka tattauna muhimman batutuwan da suka shafi zaɓe.
Gwamnan Kano ya naɗa Bilkisu Maimota a matsayin shugabar ma’aikata ta jiha
A wata sanarwa da Kwamishinan ƙasa kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu zaɓe, Mohammed Haruna, ya fitar, ya ce hukumar ta amince da ɗage aikin har sai bayan zaɓen 2027.
Sai dai INEC ta jaddada cewa aikin sabunta rajistar na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da sahihancin rijistar masu zaɓe, domin yana taimakawa wajen tantance bayanai, gyara kurakurai, cire maimaitattun sunaye da waɗanda ba su cancanta ba, tare da ƙarfafa ingancin bayanan masu zaɓe.
Hukumar ta kuma ce aikin zai bai wa masu rajista damar sabunta bayanansu idan aka fara gudanar da shi nan gaba.
