Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta dakatar da shirin ƙara kuɗin rajistar jarabawar kammala sakandare ta WAEC da NECO da aka shirya fara aiwatarwa daga shekarar 2027, domin ba da damar ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki a fannin ilimi
Daga Zainab Kamal Ibrahim
A baya dai, Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta amince da ƙarin kuɗin rajistar jarabawar zuwa Naira 50,000 ga kowane ɗalibi, matakin da ya jawo ce-ce-ku-ce daga iyaye, malamai da sauran masu ruwa da tsaki. An bayyana cewa sabon tsarin zai maye gurbin tsoffin kuɗaɗen rajista na WAEC da NECO daga shekarar 2027.
https://anzowajen.com/wp-admin/post-new.php
Sai dai, bayan korafe-korafe da suka biyo baya daga ɓangarori daban-daban, gwamnatin ta sanar da dakatar da shirin domin gudanar da ƙarin tattaunawa kafin ɗaukar mataki na ƙarshe. Masana ilimi da dama sun nuna damuwa cewa karin kuɗin na iya hana ɗalibai masu ƙaramin ƙarfi damar ci gaba da karatu.
Tun da farko, ƙarin kuɗin jarabawar ya haddasa suka daga wasu manyan ‘yan siyasa da ƙungiyoyi, waɗanda suka bayyana cewa hakan zai ƙara yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a Najeriya.
