Kanal Mohammed Ma’aji, wani jami’in Sojin Najeriya da ake zargi da hannu wajen shirya wani yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ce abin da ya sa ya shiga cikin shirin shi ne kishin ƙasa da damuwa kan halin da Najeriya ke ciki, ba neman mulki ko wata fa’ida ta kashin kai ba.
Daga Zainab Kamal Ibrahim
Ma’aji ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da bayanansa kan zargin yunkurin juyin mulkin, inda ya ce matsin tattalin arziki, rashin ingantaccen shugabanci da kuma tabarbarewar jin daɗin ’yan Najeriya da jami’an tsaro sun taimaka wajen haifar masa da damuwa kan makomar ƙasar.
Ya ce abubuwan da suka faru sun samo asali ne tun da dadewa, yana mai jaddada cewa kishin ƙasa da ƙaunar aikinsa a matsayin soja ne suka kasance daga cikin abubuwan da suka sa ya ɗauki matakin.
«“Abin da ya faru yana da dogon tarihi, kuma kishin ƙasa da ƙaunar aikina da ƙasata ne suka motsa ni,” in ji Ma’aji, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.»
Jihar Kano Ta Shiga Cikin Jerin Manyan Biranen Duniya 10 Masu Yawan Jama’a
Kanal Ma’aji ya ce yana kallon yadda matsalolin ƙasar ke ƙaruwa daga lokaci zuwa lokaci, yana mai cewa hakan ya sa yake fargabar Najeriya na iya shiga wani mawuyacin hali idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba.
Ya kuma bayyana cewa irin wannan damuwa ta shafi rayuwarsa ta yau da kullum, musamman yadda yake fama da ƙalubalen kula da ’ya’yansa biyar da albashinsa.
“Duk lokacin da na kalli yadda nake fama da wahalar rainon ’ya’yana biyar da ƙaramin albashina, ina cikin damuwa,” in ji shi.
Jami’in ya ce abin da ya fi damunsa shi ne yadda ake kula da jami’an soji, musamman waɗanda suka samu raunuka a fagen daga.
Ya yi zargin cewa wasu daga cikin sojojin da suka samu raunuka kuma ke jinya a Asibitin Kula da Sojoji na 44 da ke Kaduna, ba sa samun kulawar da ta dace, yana mai cewa wannan na daga cikin manyan matsalolin da ke addabar rundunar sojin ƙasar.
Ma’aji ya ce waɗannan matsaloli ne suka ƙara masa ƙwarin gwiwar ganin cewa akwai buƙatar ɗaukar matakan gaggawa domin sauya tafiyar ƙasar.
Ya ce manufar abin da ake zarginsa da shiryawa ita ce samar da Najeriya mai wadata da za ta zama abin alfahari ga ’yan ƙasarta.
“Manufar wannan mataki ita ce samun ƙasa mai wadata wadda dukkanninmu za mu yi alfahari da ita. Na kai wani mataki da na fara tunanin cewa idan ba a yi wani abu ba, nan gaba ƙila ba za mu sami ƙasar da za mu kira tamu ba,” in ji shi.
Sai dai Ma’aji ya ce shirin bai kai matakin aiwatar da juyin mulkin ba a lokacin da aka kama shi.
A cewarsa, an fara ƙoƙarin haɗa jami’an soji masu irin wannan tunani ne, amma har yanzu ba a kammala kafa ƙungiyar ba, kuma ba a sanya ranar aiwatar da shirin ba.
Ya kuma ce an shirya gudanar da wasu ƙarin taruka domin tattauna matakan da za a ɗauka, amma kama shi ya dakatar da tsarin.
Kanal Ma’aji ya ce shi ne ya ɗauki nauyin wasu daga cikin kuɗaɗen da ake zargin an kashe wajen shirin, yayin da Timipre Silva ya bayar da gudunmawar kusan Naira miliyan 400.
Ya musanta cewa akwai wata ƙasa ko ƙungiya ta ƙetare da ta shiga cikin lamarin, tare da cewa ba a kammala tsara ranar aiwatar da abin da ake zargin an shirya ba.
Haka kuma, ya nemi a samar da wata hanya ta musamman da jami’an soji za su iya gabatar da korafe-korafensu ga Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Waidi Shaibu, ba tare da fargabar fuskantar hukunci ko tsangwama ba.
Daga cikin shawarwarinsa akwai inganta albashi da jin daɗin jami’an tsaro, ƙara inganta tsarin fansho, ilimi da kuma ɗaukar matakan yaƙi da cin hanci da rashawa a cikin ƙasa da rundunar soji.
Ya kuma soki yadda aka cire tallafin man fetur, yana mai cewa kamata ya yi a bi tsarin cire tallafin a hankali domin rage wa ’yan Najeriya radadin sauyin.
A ƙarshe, Ma’aji ya roƙi hukumomin ƙasar da su yi masa da sauran waɗanda ake zargi da hannu a lamarin sassauci, yana mai cewa kama shi da binciken da aka gudanar sun sa ya sake duba matsayinsa.
Ya ce idan aka sake shi kuma aka ci gaba da fuskantar matsalolin da yake ganin suna addabar ƙasar, zai nemi wata hanyar daban ta bayyana damuwarsa.
“Ba mu da wata ƙasa illa Najeriya, kuma ba mu da wani aiki illa aikinmu. Wannan lamari ya buɗe mana ido kuma ya sauya tunaninmu. Ba manufarmu ba ce mu dagula zaman lafiyar ƙasar. Abin da muka yi ya samo asali ne daga kishin ƙasa, ƙaunar Najeriya da kuma burin ganin ƙasar ta bunƙasa,” in ji shi.
Rahotanni sun ce zargin yunkurin juyin mulkin ya fito fili ne a watan Satumban 2025, lamarin da ya haifar da soke bikin ranar samun ’yancin kan Najeriya na ranar 1 ga Oktoba tare da sauye-sauye a manyan mukaman rundunar sojin ƙasar.
