DAGA ZAINAB KAMAL IBRAHIM
Wata mata mai shekara 28 mai suna Firdausi Musa tare da ’ya’yanta biyu ƙanana sun jikkata sakamakon mummunar ƙona da suka samu bayan da ake zargin kishiyarta, Maryam Muhammad, ta zuba musu fetur tare da banka musu wuta a unguwar Hotoro da ke cikin birnin Kano.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan wata hatsaniya da ta ɓarke tsakanin matan biyu, inda ake zargin Maryam ta kai harin ne cikin fushi. Makwabta sun ce sun yi gaggawar kai ɗauki bayan jin ihun waɗanda abin ya shafa, kafin a garzaya da su zuwa asibiti domin samun kulawar likitoci.
NAPTIP ta ceto mutum 15 daga hannun ‘masu safarar mutane’ a Nasarawa
Jami’an tsaro sun tabbatar da faruwar lamarin, inda suka ce an kama wacce ake zargi domin gudanar da bincike kan abin da ya faru. Haka kuma, hukumomi sun yi kira ga ma’aurata da su guji rikice-rikicen cikin gida tare da neman hanyoyin sasanci maimakon ɗaukar matakan da ka iya jawo asarar rayuka.
