Zainab Kamal Ibrahim
A ranar Lahadin nan ne ake sa ran jirgin farko na maniyyata aikin Hajjin bana ta shekarar (2026) na ƙasar zai tashi zuwa Saudiyya arabiyya don gudanar da aikin Hajjin bana.
Hukumar alhazan ta ƙasar nan NAHCON, ta ce an kammala dukkan shirye-shirye da Ake gudanarwa don gudanar da jigilar maniyyata cikin nasara.
Hukumar ta ja hankalin maniyyatan ƙasar nan kan abubuwan da ya kamata su kiyaye, domin kauce wa matsala a ƙasar ta Saudiyya.
Tin da fari, mataimakiyar Darakta Fatima Sanda Usara,ta ce a sashen yada labaran hukumar, ta ce kawo yanzu hukumar na ci gaba da raba katin shaidar aikin Hajji ga maniyyata, musamman a Abuja, da Legas.
BBC
